Nigerian news All categories All tags
Wasu mahara sanye da kayan sojoji sun kashe mutum 6, sun jikkata 4 a Kaduna

Wasu mahara sanye da kayan sojoji sun kashe mutum 6, sun jikkata 4 a Kaduna

Wasu 'yan bindigar da ake kyautata zaton makiyaya ne a ranar Alhamis din da ta gabata a lokuta daban daban sun farwa wasu kauyukan da suka hada da Baking Kofi da kuma Kaninkon dukkan su a karamar hukumar Jema'a ta jihar Kaduna inda kuma suka kashe mutum shidda tare da jikkata wasu hudu.

Kamar yadda muka samu, 'yan bindigar da majiyar mu ta bayyana cewa sun kai su 10 sanye da kayan sojoji ne dai suka farma kauyukan tare da yin wannan danyen aika-aika da tsakar dare.

Wasu mahara sanye da kayan sojoji sun kashe mutum 6, sun jikkata 4 a Kaduna

Wasu mahara sanye da kayan sojoji sun kashe mutum 6, sun jikkata 4 a Kaduna

KU KARANTA: Kwace gidaje: Patience Jonathan ta mayar da martani

Legit.ng ta samu cewa wannan dai na faruwa ne duk kuwa da wani muhimmin taron masu ruwa da tsaki da aka kan yi domin lalubo hanyar da za'a kawo karshen kashe-kashen.

A wani labarin kuma, Dan tsohon gwamnan daya daga cikin jihohin Najeriya na shiyyara kudu maso yammacin Najeriya ya gurfana a gaban kotun majistare ta garin Legas bisa zargin sa da almundahana ta makudan kudaden da suka kai Naira miliyan 40.

Dan tsohon gwamnan mai shekaru akalla 40 a duniya, kamar yadda muka samu sunan sa Akinkunle Olunloyo kuma yana sana'ar gudanar da gidan rawa ne kuma 'yan sandan Najeriya ne suka gurfanar da shi a gaban kotun.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel