Nigerian news All categories All tags
Ta fito fili: Dalilin da ya sa Oyegun ya janye kudurin sa na sake tsayawa takarar shugaban APC

Ta fito fili: Dalilin da ya sa Oyegun ya janye kudurin sa na sake tsayawa takarar shugaban APC

Kamar dai yadda muka samu tabbaci daga majiyar mu, babban dalilin da ya sa shugaban jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC), Chief John Odigie-Oyegun ya janye kudurin sa na sake tsayawa takara shine ganawar da sukayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tun farko dai, kamar yadda muka samu, gwamnonin jam'iyyar sun shaidawa Cif Oyegun din ra'ayin shugaban kasa na kin goyon bayan na sa a zaben gangamin mai zuwa amma bai yadda ba har saida ya gana da shugaban da kan sa.

Ta fito fili: Dalilin da ya sa Oyegun ya janye kudurin sa na sake tsayawa takarar shugaban APC

Ta fito fili: Dalilin da ya sa Oyegun ya janye kudurin sa na sake tsayawa takarar shugaban APC

KU KARANTA: "Mulkin Buhari ne ya sa na sayar da diya ta"

Legit.ng ta samu dai cewa ana sa ran tsohon gwamnan jihar Edo ne Kwamared Adams Oshiomole zai gaje shi biyo bayan cikakken goyon bayan da yake ta samu daga manyan jam'iyyar ta APC.

A wani labarin kuma, Yayin da dukkan ma'aikata a fadin kasar nan musamman ma na gwamnati ke ta bukukuwan zagayowar ranar su a Najeriya, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma fitaccen dan siyasar nan Alhaji Atiku Abubakar ya bukaci kungiyoyin kwadago da su nemi karin albashi daga gwamnati.

Kamar dai yadda muka samu, a sakon da ya aike ga ma'aikatan, fitaccen dan siyasar da yanzu haka ke zaman dan takarar tikitin zama shugaban kasar Najeriya ya shawarci kungiyoyin da su cigaba da bukatar kyautatuwar rayuwa daga gwamnatin a dukkan fannoni.

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel