Nigerian news All categories All tags
Zan so na kawo ziyarar ban girma Najeriya - Inji Trump

Zan so na kawo ziyarar ban girma Najeriya - Inji Trump

- Shuagabn kasar Amurka Donald Trump a ranar Litinin yace zaiso ya ziyarci Najeriya,bayan ya misalta ta a matayin kasa mai dadin ziyarta

- Trump yace kamar yadda ya samu labari cewa Najeriya kas ace mai kyau da dadin ziyarta wadda babu kamarta

- Trump ya karbi bakunci shugaba Buhari lokacin da ya karbi bakuncinsa a matsayin shugaban kasar dake kusa da sahara a karo na farko

Shuagabn kasar Amurka Donald Trump a ranar Litinin yace zaiso ya ziyarci Najeriya,bayan ya misalta ta a matayin kasa mai dadin ziyarta.

Trump yace kamar yadda ya samu labari cewa Najeriya kasace mai kyau da dadin ziyarta wadda babu kamarta, ya bayyan haka ne lokacin da yake karbar bakuncin shugaba Buhari a fadar shugaban kasa a Amurka.

Trump ya karbi bakunci shugaba Buhari lokacin da ya karbi bakuncinsa a matsayin shugaban kasar dake kusa da sahara a karo na farko. Shuwagabannin sun jaddada cewa akwai bukatar kara inganta kasuwanci, fasaha da kuma hakkin dan adam.

Zan so na kawo ziyarar ban girma Najeriya - Inji Trump

Zan so na kawo ziyarar ban girma Najeriya - Inji Trump

Shugaba Buhari yayi godiya game da yanda shugaba Trump ya bayyana Najeriya a matsayi kasa mai kyau, amma dai bai bayyana cewa ko zai gayyaceshi yazo Najeriya ba. Ya bayyana hakan ne lokacin da shugaba Trump ya bayyana rashawar Najeriya a matsayin gagaruma.

KU KARANTA KUMA: Najeriya sananna ce ta bangaren rashawa - Trump

A baya Legit.ng ta kawo cewa, Donald Trump yace Najeriya sananniya ce ta fannin rashawa a lokacin ganawarsu da shugaba Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel