An kama dan tsohon gwamna a Najeriya tsamo-tsamo cikin badakalar Naira miliyan 40

An kama dan tsohon gwamna a Najeriya tsamo-tsamo cikin badakalar Naira miliyan 40

Dan tsohon gwamnan daya daga cikin jihohin Najeriya na shiyyara kudu maso yammacin Najeriya ya gurfana a gaban kotun majistare ta garin Legas bisa zargin sa da almundahana ta makudan kudaden da suka kai Naira miliyan 40.

Dan tsohon gwamnan mai shekaru akalla 40 a duniya, kamar yadda muka samu sunan sa Akinkunle Olunloyo kuma yana sana'ar gudanar da gidan rawa ne kuma 'yan sandan Najeriya ne suka gurfanar da shi a gaban kotun.

An kama dan tsohon gwamna a Najeriya tsamo-tsamo cikin badakalar Naira miliyan 40

An kama dan tsohon gwamna a Najeriya tsamo-tsamo cikin badakalar Naira miliyan 40

KU KARANTA: Tsigewa: Buhari zai san makomar sa ranar Laraba

Legit.ng ta samu cewa, dan sanda mai gabatar da kara dai tun farko ya shaidawa kotun cewa Mista Akinkunle Olunloyo ya yaudari hukumar bayar da lamuni ne inda ya karbi bashin kudaden amma kuma daga baya ya karkatar da su.

A wani labarin kuma, Wani matashi mai akalla shekaru 32 a duniya dan kasar Ghana dake aiki a wani banki ya ankarar da jama'a yadda ya ga jami'an 'yan sandan kasar na anfani da motar sa da 'yan fashi suka kwace masa tare da kusan halakashi shekaru kimanin biyu da suka shude.

Matashin mai suna Samuel Forson ya ayyana cewa a shekarar 2015 ne dai wasu 'yan fashin da ba'a san ko suwaye ba suka tare shi suka kuma kwace masa kwamfutar sa da motar sa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel