Nigerian news All categories All tags
Mafi karancin albashi na Naira dubu 18 abun kunya ne - Atiku

Mafi karancin albashi na Naira dubu 18 abun kunya ne - Atiku

Yayin da dukkan ma'aikata a fadin kasar nan musamman ma na gwamnati ke ta bukukuwan zagayowar ranar su a Najeriya, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma fitaccen dan siyasar nan Alhaji Atiku Abubakar ya bukaci kungiyoyin kwadago da su nemi karin albashi daga gwamnati.

Kamar dai yadda muka samu, a sakon da ya aike ga ma'aikatan, fitaccen dan siyasar da yanzu haka ke zaman dan takarar tikitin zama shugaban kasar Najeriya ya shawarci kungiyoyin da su cigaba da bukatar kyautatuwar rayuwa daga gwamnatin a dukkan fannoni.

Mafi karancin albashi na Naira dubu 18 abun kunya ne - Atiku

Mafi karancin albashi na Naira dubu 18 abun kunya ne - Atiku

KU KARANTA: Dalilin da ya sa Obasanjo da Babangida ba su son Buhari - Ganduje

Legit.ng ta samu Atiku Abubakar ya kuma bayyana mafi karancin albashi na Naira dubu 18 a matsayin keta kawai da tsabar mugunta domin a cewar sa yayi kadan matuka.

A wani labarin kuma, Kamar dai yadda muka samu tabbaci daga majiyar mu, babban dalilin da ya sa shugaban jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC), Chief John Odigie-Oyegun ya janye kudurin sa na sake tsayawa takara shine ganawar da sukayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tun farko dai, kamar yadda muka samu, gwamnonin jam'iyyar sun shaidawa Cif Oyegun din ra'ayin shugaban kasa na kin goyon bayan na sa a zaben gangamin mai zuwa amma bai yadda ba har saida ya gana da shugaban da kan sa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel