Nigerian news All categories All tags
Najeriya sananna ce ta bangaren rashawa - Trump

Najeriya sananna ce ta bangaren rashawa - Trump

- Shugaban kasar Amurka Donald Trump, lokacin da ya karbi bakuncin shugaba Buhari a fadarsa yace Najeriya tana da babbar matsala ta rashawa

- Najeriya sananniya ce ta fannin rashawa inji Donald Trump, ya jaddada haka ne lokacin da yake tare shugaba Buhari a kasar Amruka, yace mun tattauna game da hakan kuma mun amince zamuyi kokarin magance matsalar

- Shugaba Buhari bai musawa jawabin Donald Trump ba, wanda shima yasha fada a cikin jama’a, kuma ya nuna jin dadinsa game da nuna damuwarsa akan matsalar da shugaba Trump yayi

Shugaban kasar Amurka Donald Trump, lokacin da ya karbi bakuncin shugaba Buhari a fadarsa yace Najeriya tana da babbar matsala ta rashawa.

Najeriya sananniya ce ta fannin rashawa inji Donald Trump, ya jaddada haka ne lokacin da yake tare shugaba Buhari a kasar Amurka, yace “mun tattauna game da hakan kuma mun amince zamuyi kokarin magance matsalar.”

Shugaba Buhari bai musawa jawabin Donald Trump ba, wanda shima yasha fada a cikin jama’a, kuma ya nuna jin dadinsa ga kasar ta Amruka game da yanda shugaban kasar Trump ya nuna damuwarsa akan matsalar ta Najeriya.

Shuagab Buhari yace gwamnatinsa tayi kokari sosai wajen ganin ta magance cin mutuncin dan adam a Najeriya, musamman game yaki da kungiyar Boko Haram da ake fama dashi a yanzu.

Najeriya sananna ce ta bangaren rashawa - Trump

Najeriya sananna ce ta bangaren rashawa - Trump

Buhari ya kara da cewa bashi da wata damuwa ga kasancewar sojojin kasar Amruka a Najeriya, saboda zasuzo ne kawai domin su bayar da horo ga sojojin Najeriya da kuma taimakawa wurin cin nasarar yaki da ta’addanci a kasar.

KU KARANTA KUMA: Shugaban Amurka Trump ya koka da kashe Kiristoci a Najeriya (Bidiyo)

Kusan dai wannan ne karon farko da Shugaban kasar Bakar Afrika ya gana da Shugaban na Amurka Donald tun da yau mulki. Shugaba Buhari ya kuma yabawa kokarin da kasar Amurka take yi wajen yaki da ta’addanci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel