Nigerian news All categories All tags
Jiga-jigan jam'iyyar APC sun kauracewa yiwa shugaba Buhari yakin neman zabe

Jiga-jigan jam'iyyar APC sun kauracewa yiwa shugaba Buhari yakin neman zabe

- An bayyana wasu :?'ya'yan jam'iyyar APC da suka kewayewa shiga yiwa Buhari yakin neman zabe a matsayin masu cin dunduniyar jam'iyyar

- Gwamnan jihar Adamawa da jami'an gwamnatin sa da dama sun kauracewa kaddamar da yakin neman zaben Buhari a jihar

- Kazalika shugabannin jam'iyyar masu barin gado basu halarci taron ba

Wasu 'yan jam'iyyar APC a jihar Adamawa sun bayyana 'ya'yan jam'iyyar da basu halarci taron yakin neman zaben Buhari ba da cewar suna cin dunduniyar jam'iyyar.

Jaridar Guardian ta rawaito cewar gwamnan jihar Adamawa, Mohammed Jibrilla Bindow, da jami'an gwamnatin sa basu halarci wurin taron kaddamar da yakin neman zaben Buhari ba da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawan, zai jagoranta.

Jiga-jigan jam'iyyar APC sun kauracewa yiwa shugaba Buhari yakin neman zabe

Jibrilla Bindow

Ana alakanta rashin ganin gwamnan da adawa da sake yin takarar Buhari.

Jaridar ta wallafa cewar, Babachir, ya gargadi masu niyyar yin magudi a zaben wakilan jam'iyyar da su hakura domin hakar su ba zata cimma ruwa ba.

DUBA WANNAN: Abinda zai warware matsalolin tsaron Najeriya fiye da amfani da karfin hukuma - Tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon

A kwanakin baya jam'iyyar APC a jihar Adamawa tayi gargadin cewar jam'iyyar zata fuskanci babban kalubale matukar bata hakura da batun sake zaben sabbin shugabanni ba.

Jigo a jam'iyyar APC a jihar Adamawa, Alhaji Ahmed Lawan, ya ce tabbas akwai matsaloli cikin jam'iyyar APC tare da yin kira ga uwar jam'iyya da tayi duba na tsanaki a kan matsalolin da jam'iyyar ke tunkara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel