Nigerian news All categories All tags
Hukumar NASG ta haramta kasuwanci da talla a hanyar babban titin Karu-Abuja

Hukumar NASG ta haramta kasuwanci da talla a hanyar babban titin Karu-Abuja

Hukumar dake da alhakin kula da mayar day an kasuwa babban kasuwar Muhammadu Buhari International Market, Karu, a jihr Nasarawa ta hana kasuwanci da talla a babban titin Keffi-Karu-Abuja.

Mista Stanley Buba, shugaban hukumar ya sanar da hakan a ranar Litinin a Karu, lokacin wani ganawa da jami’an kungiyar yan kasuwa da kuma ma’aikatan sufurin hanya.

Buba wanda ya kuma kasance babban hadimin Gwamna Umaru Almakura ya bukaci yan kasuwan da su koma babban kasuwa Muhammadu Buhari dake Karu, domin habbaka kasuwanci da kuma inganta kudin shiga na jihar.

Ya yi gargadin cewa duk wanda ya taka wannan doka zai fuskanci shari’a, sannan ya shawarci yan kasuwan da suyi amfani da wannan daman a kasuwar ajen inganta kasuwancinsu, yaki da talauci da kuma kawo karshen kasuwanci.

Hukumar NASG ta haramta kasuwanci da talla a hanyar babban titin Karu-Abuja

Hukumar NASG ta haramta kasuwanci da talla a hanyar babban titin Karu-Abuja

Buba ya bayyana cewa haramcin zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Mayu.

Ya kuma gargadi direbobin haya da su daina faki yadda bai kamata ba cewa duk wanda aka kama zai fuskanci kora.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu ta bayar da umurnin karbe gidajen Patience Jonathan na birnin tarayya

A nasa martanin Alhaji Shammasu Dantsoho, shugaban kungiyar yan kasuwan jihar Nasarawa yayi alkawarin bayar da hadin kai tare da kafa kungiya domin tabbatar da tsaftar kasuwan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel