Nigerian news All categories All tags
Kungiyar cigaban Najeriya karkashi jagorancin Obasanjo sunyi Allah wadai da kamfen din Buhari duk da kashe-kashen da akeyi a kasar

Kungiyar cigaban Najeriya karkashi jagorancin Obasanjo sunyi Allah wadai da kamfen din Buhari duk da kashe-kashen da akeyi a kasar

- Kungiyar cigaban Najeriya a karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, sunyi maganaganu game da yanda Buhari ke kamfen duk da kisan da akeyi a jihohi daban daban

- Buhari ya bayyana bukatarsa ta sake tsaywa takara a shekarar 2019 bayan watanni da akayi ana jiran tsammani

- Mai magana da yawun kungiyar Akin Osuntokun, yace Buhari ya ziyarci Bauchi don yayi kamfen bayan kasa da awowi 24 da aka kashe mutane da dama a jihar Binuwai

Kungiyar cigaban Najeriya a karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, sunyi maganaganu game da yanda Buhari ke kamfen duk da kisan da akeyi a jihohi daban daban a fadin kasar.

Buhari ya bayyana bukatarsa ta sake tsayawa takara a shekarar 2019, bayan watanni da akayi ana jiran tsammani. Mutane da dama na zarginsa da kin dakatar da kisa a wasu jihohi kamar su Zamfara, Filato, Kogi, Borno, da sauransu kafin ya shiga hidimar siyasar badi.

Mai magana da yawun kungiyar Akin Osuntokun, yace Buhari ya ziyarci Bauchi don yayi kamfen bayan kasa da awowi 24 da aka kashe mutane da dama a jihar Binuwai, wanda hakan na nuna rashin tinani irin nasa

Kungiyar cigaban Najeriya karkashi jagorancin Obasanjo sunyi Allah wadai da kamfen din Buhari duk da kashe-kashen da akeyi a kasar

Kungiyar cigaban Najeriya karkashi jagorancin Obasanjo sunyi Allah wadai da kamfen din Buhari duk da kashe-kashen da akeyi a kasar

Kungiyar tayi jawabi game da rahoton bangaren Ofishin jiha na kasar Amurka, wadda a satin da ya gabata ta zargi shugaba Buhari da gazawa wurin magance rashawa a kasarda kuma taka hakkin dan adam.

KU KARANTA KUMA: Sanata ya matsa game da shawarar tsige Buhari

Haka zalika tayi magana game da yanda aka kasa kiran Sanata mai wakiltar Kogi, Dino Melaye, bayan kamun da akayi mas aba kan ka’ida ba, hakan na nuna cewa Buhari na tafiyar da mulkinsa kamar na tsohon shugaban kasa Francois Duvalier na kasar Haiti.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel