Nigerian news All categories All tags
Wadanda suka ce kada Buhari ya sake tsayawa takara a zaben 2019 masu sonsa ne – Jigon Arewa

Wadanda suka ce kada Buhari ya sake tsayawa takara a zaben 2019 masu sonsa ne – Jigon Arewa

- Sakataren jagorori a Arewa da kuma kungiyar masu ruwa da tsaki a Arewa Dr. Umar Ardo, ya duba yaga cewa wadanda ke cewa kada Buhari ya tsaya takara a zabe na gaba sun fada masa gaskiya

- Ardo yace abubuwan da ya aikata a lokacin da yake shugaban kasa a mulkin soja sune yanzu suke dawowa suna farautarsa

- Ardo da yake magana game da ganawar Buhari da Trump wadda zasuyi a ranar Litinin, yayi kira ga Trump da ya yiwa shugaba Buhari tambaya game da yanda gwamnatinsa ta zamanin soja ta daure wata ‘yar kasar Amurka

Sakataren jagorori a Arewa da kuma kungiyar masu ruwa da tsaki a Arewa Dr. Umar Ardo, ya duba yaga cewa wadanda ke cewa kada Buhari ya tsaya takara a zabe na gaba sun fada masa gaskiya. Saboda haka ya umurce shi da ya sauraresu.

Ardo yace abubuwan da ya aikata a lokacin da yake shugaban kasa a mulkin soja sune yanzu suke dawowa suna farautarsa, ya bayyana hakanne a ranar Lahadi, lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin tarayya.

Wadanda suka ce kada Buhari ya sake tsayawa takara a zaben 2019 masu sonsa ne – Jigon Arewa

Wadanda suka ce kada Buhari ya sake tsayawa takara a zaben 2019 masu sonsa ne – Jigon Arewa

Ardo da yake magana game da ganawar Buhari da Trump wadda zasuyi a ranar Litinin, yayi kira ga Trump da ya yiwa shugaba Buhari tambaya game da yanda gwamnatinsa ta zamanin soja ta daure wata ‘yar kasar Amurka, Mahmet Ben Chembi, har na tsawon shekaru 95, a shekarar 1984.

Yace matar wadda harkar kasuwanci ne kadai ya kawota kasar Najeriya, amma gwamnatin shugaba Buhari ta daureta ba tare da wata shaida dake nuna cewa ta sabawa doka ba.

KU KARANTA KUMA: Sabuwar kungiyar Boko Haram ta kwace garuruwan Borno da Yobe tana karbar haraji daga mazauna garururwan

Ardo da asalin jihar Adamawa ne ya sake sanya alamar tambaya game da jerin sunayen wadanda suka saci kudaden gwamnati wanda gwamnatin tarayya ta fitar, yace watakila ma satar da akeyi a wannan gwamnatin tafi ta da kuma baza’a gane ba sai shugaban ya bar Ofishin.

Idan ba ku manta ba dai yanzu haka Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana Birnin Washington inda zai gana da Shugaban kasar Amurkan Donald Trump a makon nan game da wasu batutuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel