Nigerian news All categories All tags
Jigo a jam’iyyar PDP ya aika ma Trump wata muhimmiyar tambaya da yake so yayi ma Buhari

Jigo a jam’iyyar PDP ya aika ma Trump wata muhimmiyar tambaya da yake so yayi ma Buhari

Sakataren kungiyar masu ruwa da tsaki na Arewacin Najeriya, Dakta Uamr Ardo ya bukaci shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya tambayi shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari kan menene dalilin da yasa Buhari ya dauke yan kasar Amurka na tsawon shekaru 95 a shekarar 1995?

Vanguard ta ruwaito Umar Ardo ya bayyana Buhari ya daure Amurkawan ne a zamanin da yake mulkin Soja, daga cikinsu akwai Mahmet Ben Chembi, ba tare da wani kwakkwaran dalili ba, inda yace Buhari bai bi doka ba wajen daure su.

KU KARANTA: Rikicin BokoHaram: Obama bai baiwa Najeriya kyakkyawar gudunmuwar da muke bukata ba – Garba Shehu

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ardo ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 29 ga watan Afrilu, a yayin ganawa da manema labaru, inda yace Buhari ba mutum bane mai bin umarnin Kotu, don haka ba cikakken dan dimukradiyya bane.

Jigo a jam’iyyar PDP ya aika ma Trump wata muhimmiyar tambaya da yake so yayi ma Buhari

Trump da Buhari

A cewar Ardo, Mista Mahmet ya shigo Najeriya a lokacin da halastaccen hanya, kuma ya shigo ne da nufin gudanar da halastaccen kasuwanci, amma ya kare a gidan Kurkuku a sanadin Buhari.

“Wani attajirin dan Amurka, Mahmet Ben Chembi wanda ya shigo Najeriya da dalan Amurka miliyan 17 daga kasar Amurka, don yin kasuwanci, amma aka zarge shi da damfara, inda aka kai shi Kotun Buhari, wanda suka yanke masa hukunsin shekaru 95 a Kurkuku.

“Bugu da kari an ci shi tarar naira miliyan 500, har sai lokacin da shugaban kasa na mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wanda ya sa aka sake duba laifin da ake zargin Mahmet, inda ya sake ta. Don haka nake kira ga Trump ya tambayi Buhari dalilin kama Mahmet.” Inji shi

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel