Nigerian news All categories All tags
A kokarin da akeyi na tsige Buhari daga mulki, fadar shugaban kasa na harin Sanatoci 15 akan zargin aikata rashawa

A kokarin da akeyi na tsige Buhari daga mulki, fadar shugaban kasa na harin Sanatoci 15 akan zargin aikata rashawa

- Wasu daga cikin yan majalisar dokoki na yunkurin tsige shugaban kasa Buhari

- Yan majalisan sunyi wannan yunkuri ne saboda biyan dala miliyan 496 na siya jirgin yaki kiran TUCANO da akayi ba bisa ka’ida ba

- Wani rahoto da ba’a tabbatar ba ya nuna cewa babu mamaki fadar shugaban kasa na harin sanatoci 15 kan zargin aikata rashawa sakamakon wannan yunkuri

Wasu daga ckin ‘yan majalisa na kokarin kawo shawarar tsige shugaba Muhammadu Buhari daga bisa kan mulki, saboda ya cire kudi ba tare da izinin majalisa ba.

‘Yan majalisar sunyi wannan yunkurin hakanne sakamakon wasu kudade $496m na sayen jiragen yaki na TUCANO da shugaban ya cire daga asusun gwamnati bada izininsu ba, duk da dai shi ya hangi cewar bazasu ki amince mas aba shiyasa ya aikata hakan.

Fadar shugaban kasa na harin wasu sanatoci 15 da aikata rashawa, sakamakon kawo shawarar tsige shugaban kasar da sukayi yunkurin kawo shawara akai.

A kokarin da akeyi na tsige Buhari daga mulki, fadar shugaban kasa na harin Sanatoci 15 akan zargin aikata rashawa

A kokarin da akeyi na tsige Buhari daga mulki, fadar shugaban kasa na harin Sanatoci 15 akan zargin aikata rashawa

Legit.ng ta ruwaito cewa Sanata Mathew Urhoghide ya gardanta kawo shawarar tsige Buhari daga kan mulki da akace yayi, ya gardanta hakan ne lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a filin jirgi na Benin dake jihae Edo.

KU KARANTA KUMA: Bazamu taba yin shugaban kasar da ba zai iya zuwa Amurka ba – Lauretta Onochie

Sanatocin dake fuskantar tuhume-tuhume sun hada da Sanata Dino Melaye, Sanata Shehu Sani , Sanata Isa Misau, Sanata Abdullahi Adamu, Sanata Peter Nwaoboshi , Sanata Danjuma Goje, Aliyu Wamakko, Murtala Nyako, Jonah Jang, Ike Ekweremmadu , Bukola Abubakar Saraki da kuma Sanata Rabiu Musa Kwakanso.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wasu sanatoci sun bukaci a tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari sakamakon cire kudin siyar jirgin yaki da yayi ba tare da yardar su ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel