Nigerian news All categories All tags
‘Yan Sanda 30 ke zagaye da asibitin da Dino Melaye ya ke jinya

‘Yan Sanda 30 ke zagaye da asibitin da Dino Melaye ya ke jinya

- Jami’an tsaro sun zagaye asibitin da aka kwantar da Sanata Dino Melaye

- An rahoto cewa yanzu haka ‘Yan Sanda akalla 30 ne ke sinitiri a asibitin

- 'Dan Majalisar yayi kokarin kufcewa ‘Yan Sanda kwanaki sai yayi hadari

Yanzu haka da mu ke magana Jami’an tsaro rututu na gadin Sanatan Kogi ta Yamma Dino Melaye a gadon asibiti a Birnin Tarayya Abuja kamar yadda labari ya zo mana daga Jaridar Daily Trust ta kasar.

‘Yan Sanda 30 ke zagaye da asibitin da Dino Melaye ya ke jinya

Dino Melaye na shan tsaron 'Yan Sanda a asibiti

Sojoji akalla 30 ne ke tsare da Fitaccen ‘Dan Majalisar inda yake jinya a Abuja. Idan ba ku manta ba kwanaki ‘Yan Sanda su kayi kokarin kama Sanatan inda shi kuma ya duro daga cikin motar su har ya samu rauni.

KU KARANTA: Zaman kadaici ya sa tsofaffin yin sata a wata kasa

‘Yan Jarida sun samu asibitin a zagaye da Jami’an tsaro lokacin da su ka kai ziyara. An baza ‘yan Sanda rike da makamai a gaban asibitin da kuma cikin sa har da waje. Ko ta ina dai Jami’an tsaro ne ke sinitiri a asibitin.

Ta dai kai kafin mutum ya shiga cikin asibitin mai hawa 4 sai ya bi ta gaban wasu manyan Jami’an Sojoji 3. Jami’an Sojojin kuma su na binciken motocin da ke shigowa kamar yadda Jaridar ta Daily Trust ta bayyana.

Dama kun ji cewa yanzu haka dai Sanatan na kwance a wani ‘daki na musamman an katange sa daga sauran jama’a. Ba dai kowa ake bari ya shigo asibitin ba tun lokacin da aka kwantar da ‘Dan Majalisar a makon jiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel