Nigerian news All categories All tags
Majalisa ba ta da ikon aikawa Shugaban kasa sammaci -Masana tsarin mulki

Majalisa ba ta da ikon aikawa Shugaban kasa sammaci -Masana tsarin mulki

Wasu manyan masana harkar shari’a a kasar nan sun bayyana ce Majalisa ba ta da ikon aikawa Shugaban Kasa takarda ya bayyana a gaban ta ganin ce-ce-ku-cen da ya taso cikin ‘yan kwanakin nan.

A makon nan ne aka yi zama game da wasu kudi da Shugaban kasar ya ware domin sayen jiragen yaki ba tare da sanin Majalisa ba. Don haka ne wasu Sanatocin kasar su ka nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya zo yayi masu karin bayani.

Majalisa ba ta da ikon aikawa Shugaban kasa sammaci -Masana tsarin mulki

Lauyoyin sun ce Buhari ya fi karfin Majalisa ta kira sa

Wani rikakken Lauya wanda yak ware a harkar tsarin mulkin kasa Ben Nwabueze ya bayyanawa Daily Trust cewa duk da Shugaban kasar ya sabawa kundin tsarin mulki, Majalisar ba ta da damar kiran Shugaban kasa gaban ta don ya sha gaban ta.

KU KARANTA: Buhari ya amince ya kashe sama da Biliyan 2 a Jami’ar Maiduguri

Yato Oyetibo SAN ke cewa duk da Majalisa na da ikon kiran jama’a zuwa gaban ta, sai dai tsarin kasa bai bada dama a kira Shugaban kasa ba saboda tsarin mulki ya ba sa kariya daga wata tuhima ko sammaci daga kowace irin Hukuma ta kasar.

Shi ma dai Emeka Etiba wanda rikakken Lauyan ne, yace Majalisa tana iya sa kowa ya bayyana a gaban ta yana karkarwa amma fa ban da Shugaban kasa da kan sa don haka sai dai a tuntubi Ministocin sa idan har ana son wata amsa.

Idan ba ku manta ba dai yanzu haka Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana Birnin Washington inda zai gana da Shugaban kasar Amurkan Donald Trump a makon nan game da wasu batutuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel