2019: Shekarau ya shirya fitowa takarar shugaban kasa a PDP

2019: Shekarau ya shirya fitowa takarar shugaban kasa a PDP

- Shekarau wanda yayi ministan ilimi a lokacin mulkin PDP na Goodluck Ebele Jonathan, a wata wasika da majiyar mu Legit.ng ta samu a jiya yace ya yanke shawarar fitowa takarar shugaban kasar ne saboda kiraye - kirayen da al'ummar Najeriya keyi masa akan ya fito

2019: Shekarau ya shirya fitowa takarar shugaban kasa a PDP

2019: Shekarau ya shirya fitowa takarar shugaban kasa a PDP

Shekarau wanda yayi ministan ilimi a lokacin mulkin PDP na Goodluck Ebele Jonathan, a wata wasika da majiyar mu Legit.ng ta samu a jiya yace ya yanke shawarar fitowa takarar shugaban kasar ne saboda kiraye - kirayen da al'ummar Najeriya keyi masa akan ya fito.

DUBA WANNAN: Abubuwa na cigaba da faruwa a Saudiyya: An gabatar da wasan kokawa na 'yan Amurka wato WWE a birnin Jiddah

"Kamar yanda kuka sani, tun bayan zaben 2015, na samu kiraye kirayen mutane da wasu kungiyoyi a fadin kasar nan don in tsaya takarar shugabancin kasar nan a zabe na gaba."

"Nasan sunyi haka ne don ganin nasarorin dana samu lokacin mulkina a jihar kano (2003-2011) da kuma lokacin dana yi ministan ilimi daga watan Yuli 2014 zuwa watan Mayu 2015."

"Domin na amsa kiran ku, duk da wahalar aikin dake gabana. Na ji ra'ayoyin mutane da kungiyoyi da yawa a fadin kasar nan, a inda suka nuna amincewar su tare da bani shawarwarin da suka kamata. A sakamakon shawarwarin ne nake farincikin sanar daku cewa zan fito domin in bada gudumawa ta ga cigaban kasar nan. Na yanke shawarar amsa kiranku." inji Shekarau.

Bayyana nufin Shekarau na nuna cewa zai bi sahun su Atiku Abubakar, Governor Ibrahim Hassan Dankwambo na jihar Gombe, Ahmed Makarfi da tsohon shugaban majalisa David Mark wadanda suke neman shugabancin kasar nan karkashin jam'iyyar ta PDP.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel