Nigerian news All categories All tags
Ziyarar Amurka: Fadar Shugaban kasa tayi wa jama’a karya Inji Hadimin Jonathan

Ziyarar Amurka: Fadar Shugaban kasa tayi wa jama’a karya Inji Hadimin Jonathan

- Shugaban kasa Buhari zai gana da Donald Trump a Amurka a makon nan

- An rahoto cewa Buhari ne Shugaban Afrikan farko da zai hadu da Trump

- Hadimin Jonathan Reno Omokri yace Hadiman Buhari sun sharba karya

Yanzu haka Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana Birnin Washington DC tun jiya inda zai gana da Shugaban kasar Amurkan Donald Trump a makon nan game da wasu muhimman batutuwan da su ka shafi manyan kasashen biyu.

Ziyarar Amurka: Fadar Shugaban kasa tayi wa jama’a karya Inji Hadimin Jonathan

Ba Buhari bane wanda zai fara ganawa da Trump a Afrika

Lokacin da fadar Shugaban kasa ta sanar da ziyarar ta bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya shi ne Shugaban kasar da zai fara ganawa da Donald Trump na Amurka daga Nahiyar Afrika tun da ya hau mulki.

KU KARANTA: Buhari ya amince ya kashe sama da Biliyan 2 a Jami’ar Maiduguri

Sai dai wani tsohon Hadimin Shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi wa Fadar Shugaban kasan raddi inda yace karya ce kurum aka sharba da aka ce Shugaba Buhari ne wanda zai fara haduwa da Takwaran na sa Trump daga Kasar Afrika.

Reno Omokri a shafin sa na Tuwita yayi wa Jaridar Punch da ta dauki wannan labari gyara inda yace a shekarar bara Shugaban kasar Masar watau Abel Fatah Al-Sisi ya zanta da Donald Trump a Amurka don haka bai yiwuwa ace Buhari ne farko.

A baya dama kun ji cewa a baya Bashir Ahmad yace Shugaba Buhari ne wanda zai fara ganawa da Shugaba Trump daga cikin Shugabannin Afrika. Sai dai ba shakka wannan ne karon farko da Shugaban kasashen Bakar Fatar Afrika zai gana da Trump.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel