Sabbin masana'antun wutar lantarki 4 za su fara aiki gadan-gadan a Najeriya

Sabbin masana'antun wutar lantarki 4 za su fara aiki gadan-gadan a Najeriya

Kimanin kusan wutar lantarkin da ta kai yawan 1,262 na ma'aunin Mega wat ne zai karu a Najeriya nan da alkalla watanni hudu indai har sabbin masana'antun wutar lantarkin kasar suka soma aiki gadan-gadan.

Mun samu daga majiyar mu dai cewa kawo yanzu aski yazo gaban goshi wajen ganin cewa masana'antun wutar lantarkin wadanda dukkanin su suna a yankin Neja Delta ne za a fara aikin gwajin su ne a cikin satukan nan masu zuwa.

Sabbin masana'antun wutar lantarki 4 za su fara aiki gadan-gadan a Najeriya

Sabbin masana'antun wutar lantarki 4 za su fara aiki gadan-gadan a Najeriya

KU KARANTA: PDP ta bayar da siffofin wanda za ta ba tikitin takara da Buhari

Legit.ng dai ta samu cewa sabbin masana'antun na wutar lantarkin sun hada da ta garin Gbarain sai ta garin Aloji da kuma ta garin Omoku sannan daga karshe ta garin Afam.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Kano kuma daya daga cikin manyan magoya bayan tazarcen shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019, Alhaji Abdullahu Umar Ganduje ya bayyana cewa babban dalilin da ya ke zargin shine ya sanya tsaffin shugabannin kasar Najeriya Obasanjo da Babangida basu son shugaba Buhari.

A yayin wata fira da gwamnan yayi da majiyar mu, ya bayyana cewa saboda shugaba Buhari yana da zummar yaki da cin hanci da rashawa shi ya sanya ba su son yayi tazarce.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel