Nigerian news All categories All tags
Nasarori 3 da ko makaho ya san shugaba Buhari ya same su - Lai Mohammed

Nasarori 3 da ko makaho ya san shugaba Buhari ya same su - Lai Mohammed

Babban ministan yada labarai da al'adu na tarayyar Najeriya Alhaji Lai Mohammed ya bayyanawa al'ummar duniya baki daya cewa shugaba Muhammadu Buhari yana da cikakkiyar lafiyar da zai cigaba da jagorantar Najeriya har shekarar 2023.

Alhaji Lai Mohammed ya yi wannan ikirarin ne a yayin wata ziyarar aiki da yake kaiwa a manyan kafafen yada labarai na duniya a kasar Amurka inda ya kuma ayyana cewa shugaban ya samu nasara sosai a mulkin sa.

Nasarori 3 da ko makaho ya san shugaba Buhari ya same su - Lai Mohammed

Nasarori 3 da ko makaho ya san shugaba Buhari ya same su - Lai Mohammed

KU KARANTA: Yan majalisar tarayya 5 da suka so a tsige Buhari

Legit.ng ta samu cewa Lai Mohammed ya bayyana bangarori uku da suka hada da harkar tsaro, yakar cin hanci da rashawa da kuma samar wa da al'umma aikin yi musamman matasa a matsayin nasarorin da shugaban ya samu.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Kano kuma daya daga cikin manyan magoya bayan tazarcen shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019, Alhaji Abdullahu Umar Ganduje ya bayyana cewa babban dalilin da ya ke zargin shine ya sanya tsaffin shugabannin kasar Najeriya Obasanjo da Babangida basu son shugaba Buhari.

A yayin wata fira da gwamnan yayi da majiyar mu, ya bayyana cewa saboda shugaba Buhari yana da zummar yaki da cin hanci da rashawa shi ya sanya ba su son yayi tazarce.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel