Nigerian news All categories All tags
Batun tsigewa: Shugaba Buhari zai san makomar sa a ranar Laraba

Batun tsigewa: Shugaba Buhari zai san makomar sa a ranar Laraba

Yanzu haka dai zukatan manyan 'yan Najeriya musamman ma masu rike da madafun iko a mataki na tarayya na cike da jiran tsammani game da rahoton kwamitin majalisar dattawa ya kafa domin ya binciki badakalar siyen makamai ba bisa ka'ida ba da ake zargin shugaba Buhari yayi zai mika rahoton sa.

Kwamitin dai wanda aka dorawa alhakin yin bincike game da lamarin a satin da ya gabata game da badakalar kashe kudin da suka kai dalar Amurka miliyan 496 an ce su mika rahoton ne ranar Laraba mai zuwa.

Batun tsigewa: Shugaba Buhari zai san makomar sa a ranar Laraba

Batun tsigewa: Shugaba Buhari zai san makomar sa a ranar Laraba

KU KARANTA: Jam'iyyar PDP ta bayar da siffofin wanda za ta tsayar takara da Buhari

Legit.ng dai ta samu cewa bayanan rahoton ne zai bayar da haske game da makomar shugaban kasar.

A wani labarin kuma, Babban ministan yada labarai da al'adu na tarayyar Najeriya Alhaji Lai Mohammed ya bayyanawa al'ummar duniya baki daya cewa shugaba Muhammadu Buhari yana da cikakkiyar lafiyar da zai cigaba da jagorantar Najeriya har shekarar 2023.

Alhaji Lai Mohammed ya yi wannan ikirarin ne a yayin wata ziyarar aiki da yake kaiwa a manyan kafafen yada labarai na duniya a kasar Amurka inda ya kuma ayyana cewa shugaban ya samu nasara sosai a mulkin sa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel