Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta bayar da siffofin wanda za ta tsayar takarar shugaban kasa

Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta bayar da siffofin wanda za ta tsayar takarar shugaban kasa

Rahotannin da muke samu na nuni da cewa babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) tuni shire-shiren ta sun yi nisa wajen nemo dan takarar da zai iya doke shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Kamar dai yadda muka samu, duk da cewar jam'iyyar ta gindayawa kanta sharadin fito da dan takarar ta na shugaban kasa daga Arewa, haka ma kuma yanzu ta dukufa ne wajen ganin ta fitar da wanda bai da wata makusa.

Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta bayar da siffofin wanda za ta tsayar takarar shugaban kasa

Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta bayar da siffofin wanda za ta tsayar takarar shugaban kasa

KU KARANTA: PDP ta fara zawarcin Sanata Dino Melaye

Jam'iyyar har ila yau ta bayyana cewa dole ne wanda duk za ta ba tikitin ta to ya zama bai da wata makusa kuma ya zama wanda ba'a taba kamawa da laifi ga.

Legit.ng ta samu cewa kawo yanzu dai wasu daga cikin wadanda ke neman tikitin takarar shugabancin kasar a jam'iyyar ta PDP sun hada da Sanata Makarfi, Sule Lamido, Atiku Abubakar, Kabiru Tanimu Turaki da dai sauran su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel