Babu wanda ya isa ya koro Dino Melaye daga Majalisa – APC

Babu wanda ya isa ya koro Dino Melaye daga Majalisa – APC

Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Kwara Alhaji Haddy Ametuo yayi magana game da yunkurin da aka yi na dawo da daya daga cikin ‘Yan Majalisar Yankin Sanata Dino Melaye gida.

Haddy Ametuo yayi farin cikin ganin cewa kiranyen da aka shiryawa Sanatan Kogi ta Yamma Dino Melaye bai kai ko ina ba. Ametuo yace abin da zai faru kenan a zabe mai zuwa na 2019 game da fitaccen ‘Dan Majalisar Dattawan.

Babu wanda ya isa ya koro Dino Melaye daga Majalisa – APC

Jam'iyyar APC tace dole a zauna da Dino Melaye a Kogi

Alhaji Ametuo ya nuna cewa babu wani yunkuri da zai kai ga nasara wajen ganin an ga bayan Sanatan komai yawan kudin da aka kashe domin a danne gaskiya. Ametuo yace mutanen Jihar Kogi ta Yamma su na tare da ‘Dan Majalisar su.

KU KARANTA: 'Yan sara-suka sun tarwatsa wani taron APC a Kaduna

Haka kuma Shugaban Jam’iyyar APC ya yabawa Hukumar zabe na kasa INEC saboda rashin nuna son kai inda yace su na sa rai a 2019 ayi zabe na gari. Shugaban Jam’iyyar yayi kira da ‘Ya ‘yan su da su cigaba da fito da sunan APC.

Dama dazu kun samu labari cewa shirin da aka fara na maida ‘Dan Majalisar Dattawan da ke wakiltar Yammacin Jihar Kogi Sanata Dino Melaye gida ba zai kai ko ina ba bayan da aka gaza samun yawan sa-hannun jama’a.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel