Nigerian news All categories All tags
Yanzu-yanzu: 'Yan sara-suka sun tarwatsa taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a Kaduna, sun raunata wasu

Yanzu-yanzu: 'Yan sara-suka sun tarwatsa taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a Kaduna, sun raunata wasu

Wasu matasa da ake zargin 'yan sara-suka ne sun tarwatsa taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC bangaren Sanata Suleiman Hunkuyi, mai wakiltar jihar Kaduna ta arewa.

'Yan sara-sukan, kimanin su 10, sun dira Otal din NUT Well a garin Kaduna da misalin kafe 3:15 kuma sun hau duk wanda suka gani da sara har da wadanda suka sauka a Otal din, ba 'yan siyasa ba.

Duk da babu rahoton rasa rai, mutane biyar sun samu raunuka daban-daban kuma tuni an garzaya da su asibitin kwararru na Barau Dikko domin duba lafiyar su.

Yanzu-yanzu: 'Yan sara-suka sun tarwatsa taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a Kaduna, sun raunata wasu

Ofishin jam'iyyar APC da aka rushe a Kaduna

Kazalika 'yan dabar sun yi amfani da muggan makamai dake hannun su wajen lalata kayayyakin Otal din.

DUBA WANNAN: Bautar bishiya a Kano: An raunata 'yan Hisbah a rikicin sare ta

Jami'an tsaro sun yi harbin iska domin razana 'yan sara-sukar yayinda da yawa daga cikin 'yan siyasar da suka halarci taron sun arce domin tsira da lafiyar su.

Dama Sanata Hunkuyi ya taba zargin cewar akwai shirin hana zaben wakilan jam'iyyar da zasu zabi 'yan takara domin ana son yin rubutu ne kawai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel