Karshen alewa… Dubun wani likitan bogi ta cika a Katsina
- Komai nisan jifa, masu iya magana suka ce kasa zai fado
- Bayan shafe shekaru yana tsirawa mutane allura da kara musu jini gami da basu kwayoyi, ashe dai likitan bogi
Dubun wani likitan bogi ta cika a jihar Katsina bayan da ya shiga komar yan sanda, wanda ake zargin mai shekaru 38 ya kware a harkar sojan gona da cewa wai shi kwararren likita ne, har ma ya sha yiwa mutane allura da karin jini da ruwa balle kuma bayar da magani.
Yanzu haka dai tuni wanda ake zargin mai suna Joseph Umaru ya amsa laifinsa bayan da ya shiga hannun yan sanda.
Liktan bogin dai mazaunin unguwar Kwado ce dake karamar hukumar Kaita a cikin babban birnin na Katsina. Kuma bayanai sun nuna cewa ya shafe shekaru da dama yana basajar.
Yan sanda dai sun bayyana cewa Umaru da asalin jihar Kogi ne amma yana da mataimaka biyu masu suna Rabe Lawal mai shekaru 40 da kuma Shehu Halilu mai shekaru 37.
KU KARANTA: Za'a kwata: Bayan tsallake rijiya da baya da Sanata Melaye yayi, an sako wani Sanatan a gaba
Kakakin rundunar yan sanda ta jihar DSP Gambo Isah, ya bayyanawa majiyarmu cewa, sun samu nasarar cafke wanda ake zargin ta sandiyyar bayanan sirri, kuma sun samu kayan ayyukan asibiti masu yawa a gidansa kamar; sirinji da allurai da jinni iri-iri da kwayoyin magani da kuma takardun kamala makarantar koyan aikin lafiya ta Kankia da Funtua.
“Zamu cigaba da gudanar da bincike kuma nan ba da jimawa ba za’a gurfanar da wadanda ake zargin gaban manta sabo” a cewar DSP Isah
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku
ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng