Da dumin sa: Bam ya fashe a garin shugaban kungiyar 'yan kabilar Igbo

Da dumin sa: Bam ya fashe a garin shugaban kungiyar 'yan kabilar Igbo

An samu fashewar bam a Ukehe ta jihar Enugu, garin shugaban 'yan kabilar Igbo (Ohaneze Ndigbo), Mista John Nnia Nwodo.

Saharareporters ta rawaito cewar an wulla bam din ne gidan Mista Nwodo dake Ukehe a Enugu da ranar yau, Lahadi. Fashewar bam din ta lalata rufi da tagogin gidan da sauran bangaren ginin gidan.

Ya zuwa yanzu babu rahoton asarar rai sakamakon fashewar bam. Kazalika babu rahoton ko Mista Nwodo ko iyalin sa na cikin gidan da aka cilla bam din.

Da dumin sa: Bam ya fashe a garin shugaban kungiyar 'yan kabilar Igbo

Da dumin sa: Bam ya fashe a garin shugaban kungiyar 'yan kabilar Igbo

Hukumar 'yan sanda bata fitar da wata sanarwa dangane da harin ba.

A wani labarin mai alaka da wannan, Legit.ng ta wallafa cewar a kalla mutane tara ne wasu 'yan bindiga suka harbe a wani wurin hakar ma'adanai a kauyen Mahanga dake karamar hukumar Gwari.

DUBA WANNAN: Kuma dai: 'Yan bindiga sun kara kai hari jihar Kaduna, sun hallaka mutane 9

Mutanen tara na daga cikin mutane 11 da suka je kauyen Mahanga domin hakar ma'adanai Amma 'yan bindiga suka dirar masu tare da bude masu wuta.

Mutum biyu daga cikin mutanen sun yi nasarar tserewa cikin daji bayan an bude masu wuta kuma su ne su ka kawo labarin abinda ya faru garin Birnin Gwari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel