Nigerian news All categories All tags
Kuma dai: 'Yan bindiga sun kara kai hari jihar Kaduna, sun hallaka mutane 9

Kuma dai: 'Yan bindiga sun kara kai hari jihar Kaduna, sun hallaka mutane 9

A kalla mutane tara ne wasu 'yan bindiga suka harbe a wani wurin hakar ma'adanai a kauyen Mahanga dake karamar hukumar Gwari.

Mutanen tara na daga cikin mutane 11 da suka je kauyen Mahanga domin hakar ma'adanai a jiya, Asabar, amma 'yan bindiga suka dirar masu tare da bude masu wuta.

Kuma dai: 'Yan bindiga sun kara kai hari jihar Kaduna, sun hallaka mutane 9

Kuma dai: 'Yan bindiga sun kara kai hari jihar Kaduna, sun hallaka mutane 9

Mutum biyu daga cikin mutanen sun yi nasarar tserewa cikin daji bayan an bude masu wuta kuma su ne su ka kawo labarin abinda ya faru garin Birnin Gwari.

DUBA WANNAN: Kiranye: Dino Melaye ya mayar da martani daga gadon asibiti, ya yi godiya

Wani mazaunin garin Birnin Gwari ya shaidawa jaridar Daily Trust cewar 'yan bindigar sun kone gawar mutane biyu daga cikin masu hakar ma'adanai da suka kashe.

Kokarin jin ta bakin kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Kaduna, Mukhtar Aliyu, bai samu ba domin bai amsa kiran wakilin jaridar Daily Trust ba ya zuwa lokacin da aka buga wannan rahoto.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel