Nigerian news All categories All tags
An kuma: Obasanjo ya sake sarar Buhari da zabgegiyar adda

An kuma: Obasanjo ya sake sarar Buhari da zabgegiyar adda

- Dangantaka na kara tsamari tsakanin Obasanjo da Buhari

- Yanzu haka kungiyar da Obasanjon ya kafa ta Hadakar kungiyoyi masu son cigaban Najeriya ta kudiri aniyar ganin bayan Buhari

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya sake bayyana sukarsa a fili karara ga shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatinsa. Wannan suka dai ta baya-bayan nan na zuwa ne yayin wani taro na da kungiyar Hadakar kungiyoyi masu son cigaban Najeriya (CNM), da yake jagoranta ta gudanar a jiya Asabar a garin Oyo.

An kuma: Obasanjo ya sake sarar Buhari da zabgegiyar adda

An kuma: Obasanjo ya sake sarar Buhari da zabgegiyar adda

Taron dai ya gudana ne a filin shakatawa na Trans Amusement Park dake garin Bodija a Ibadan.

Yayin taron dai, tsohon shugaban kasar ya sanya kayan da yan kungiyar kansa na riga koriya da shudin wando tare da hula.

An kuma: Obasanjo ya sake sarar Buhari da zabgegiyar adda

An kuma: Obasanjo ya sake sarar Buhari da zabgegiyar adda

Daga cikin mahalarta taron akwai shugaban kungiyar, tsohon gwamnan jihar Osun Prince Olagunsoye Oyinlola da gwamnan jihar Oyo Ambassador Taofeek Arapaja da sauran manya-manyan mambobin kungiyar.

KU KARANTA: Dino Melaye: Maganar koro fitaccen ‘Dan Majalisar APC ta ki yiwuwa

Me kuke tsammani daga wadanda muka ce saboda sun kasa su bayar da dama ga wasu su jarraba? Tabbas zasu yake mu da duk makaman da suke da su. A saboda haka dole mu kasance cikin shiri.

Mun san abu ne mai wahala ciro kwakwa daga tushenta; haka zalika su ma su sani cewa, ba karamin aiki bane a gabansu na yiwa mutane abin da ya dace a gwamnatance.

A saboda haka dole ne ku nuna jajircewa da kuma gwarin gwuiwa, domin akwai aiki ja a gabanmu. Obasanjo ya shaidawa yan kungiyar.

An kuma: Obasanjo ya sake sarar Buhari da zabgegiyar adda

An kuma: Obasanjo ya sake sarar Buhari da zabgegiyar adda

Ya kuma shaidawa mahalarta taron, da kada su ji tsoron komai domin lallai za'a yi yunkurin tsorata su, a daidaikunsu ko da yawansu, amma shi ba abinda zai iya tsora ta shi domin yaga komai tun daga farko har karshe.

Kungiyar dai yanzu na da kusan mambobi miliyan uku a fadin kasar nan kuma tana yunkurin hada karfi da sauran jam’iyyun siyasa don tunkarar zabe mai zuwa a 2019. A cewar Oyinlola wani kusa a kungiyar.

Sukar shugaba Buhari dai ba yau Obasanjo ya fara ba, wanda har ta kai ga ya kafa Hadakar kungiyoyi masu son cigaban Najeriya da babban burinta shi ne cisge shugaba Buhari daga kan mulki tunda ya ki karbar shawarar ya hakura ta lallami.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel