Nigerian news All categories All tags
Abubuwa 4 da ya kamata ku sani dangane da ziyarar Buhari a Amurka

Abubuwa 4 da ya kamata ku sani dangane da ziyarar Buhari a Amurka

A gobe, Litinin, shugaban kasar Amurka Donald Trump zai karbi bakuncin Buhari a fadar gwamnatin sa, White House.

Shugaba Buhari ne shugaban kasar Afrika na farko da gwamnatin Trump ta gayyata zuwa fadar gwamnatin ta domin tattaunawa.

1. Yaki da ta'addanci: Najeriya ta shiga shekara ta tara tana yaki kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabas ga kuma sabon rikicin makiyaya da ya kunno kai.

Shugabannin biyu zasu tattauna hanyoyin da zasu hada karfi da karfe domin kawo karshen aiyukan ta'addanci a Najeriya.

Abubuwa 4 da ya kamata ku sani dangane da ziyarar Buhari a Amurka

Buhari da Trump

Trump ya taba sukar tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama saboda kin sayar wa da Najeriya makamai.

2. Inganta dangantaka tsakanin kasar Amurka da Najeriya da kasashen Afrika: Gayyatar shugaba Buhari wata manuniya ce cewar kasar Amurka ta yarda da cewar Najeriya ce ga kasashen Afrika.

Kalaman kaskanci da shugaba Trump ya yi a kan kasashen Afrika a watannin baya ya jayo barkewar cece-kuce da kunakuni daga shugabannin duniya da 'yan Afrika.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya yi wasu sabbin nade-nade, duba sunayen su da hukumomin zasu jagoranta

3. Tazarce: Shugaba Buhari da Trump zasu sake yin takara domin zarcewa a kan mulki. Shugaba Buhari zai yi amfani da damar ziyarar domin bayyana irin nasarorin da gwamnatin sa ta samu a bangaren noma domin samun goyon bayan kasar Amurka a zaben shekarar 2019.

4. Tattalin arziki: Kasar Amurka ta nuna damuwar ta a kwanakin baya dangane da yadda kasar China ke yunkurin mamaye kasuwancin kasashen nahiyar.

A kwanakin baya kasar Amurka ta turo tsohon sakataren gwamnatin ta, Rex Tillerson, domin nunawa kasashen Afrika illar kulla harkokin tattalin arziki a nahiyar Afrika. Saidai bai karasa ziyarar ba shugaba Trump ya kore shi daga aiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel