Nigerian news All categories All tags
Atiku ya bayar da amsa kan maganar hana shi zuwa Amurka

Atiku ya bayar da amsa kan maganar hana shi zuwa Amurka

- Atiku Abubakar ya amsa tambayar da ake cewa ta gagara ya amsa lokaci mai tsawo

- Kuma ya masa tambayar ne har da karin bayanin gidan da aka ce Amurka ta siyar nasa

- Sannan yayi gugar zana ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo

Tsohon Mataimakain shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ya ce ba lallai ne sai yaje Amurka ba sannan zai iya zama shugaban ƙasa ba.

Atiku ya bayar da amsa kan maganar hana shi zuwa Amurka

Atiku Abubakar Tsohon Mataimakin shugaban kasa

Atiku dai ya amsa tambayar da akai masa ne yayin wata hira da BBC Hausa a jiya Asabar, kan cewa, shin ina gaskiyar maganar da aka ce Amurka ta hana shi zuwa ƙasarta?

Atiku yayi bayanin cewa da gaske ne yayi niyyar zuwa Amurka, amma bai samu takardar amincewa ba (Visa) ba, amma bai san dalili ba. Sai ya tambaya ko "Kundin tsarin mulkin Najeriya ne ya ce dole sai naje Amurka kafin na iya zama shugaban ƙasa, zan iya zama shugaban ƙasa ba tare da naje Amurka ba."

KU KARANTA: Zaben Ekiti: Ana wasu gyare-gyare a Jam’iyyar APC domin a kai ga nasara Inji Ogundana

Da yake amsa tambayar ko ya yaji a ransa a lokacin da tsohon shugaban ƙasa Obasanjo ya ce, mutuƙar yana raye Atiku bai isa ya zama shugaban ƙasa ba, cewa yayi, baccinsa ya sha har da mun shari domin yasan Allah ne kaɗai ke bayar da mulki. Kuma idan Allah ya yarda, shi Obasanjo bai isa ya hana ba.

Atiku ya bayar da amsa kan maganar hana shi zuwa Amurka

Atiku ya bayar da amsa kan maganar hana shi zuwa Amurka

Yayin da aka tambaye shi man maganar sayar da gidansa da gwamnatin Amurka tayi kuwa, cewa yayi, gidan matarsa ne kuma ita taje har can ta siyar ba wai gwamnatin Amurka ce ta siyar mata ba.

Atiku ya kuma bayar da amsar tambayar dalilin raba garinsa da shugaba Muhammadu Buhari, da cewa, baya ɗaukar shawara domin bayan zaɓen 2015, sai da na same shi na faɗa masa abubuwa basa tafiya yadda ya kamata, na kuma bashi shawarar yadda ya kamata yayi amma yayi kunnen uwar shegu da ita. Wannan ne dalilin da yasa na komo jam'iyya ta ta asali PPD.

Atiku ya bayar da amsa kan maganar hana shi zuwa Amurka

Atiku ya bayar da amsa kan maganar hana shi zuwa Amurka

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel