Nigerian news All categories All tags
Zaben Ekiti: Ana wasu gyare-gyare a Jam’iyyar APC domin a kai ga nasara Inji Ogundana

Zaben Ekiti: Ana wasu gyare-gyare a Jam’iyyar APC domin a kai ga nasara Inji Ogundana

- Ana kokarin yi wa Jam’iyyar APC garambawul domin lashe zaben Ekiti

- Gwamna Ayodele P. Fayose zai bar kujerar sa bayan ya kammala mulki

- Jam’iyyar adawa na kokarin ganin dai ta koma gidan Gwamnati a Ekiti

Mun samu labari cewa wani jigo a Jam’iyyar APC mai mulki a Najeiya ya bayyana cewa Jam’iyyar na fuskantar wasu gyare-gyare yadda za ta samu nasara a zabukan kasar masu zuwa nan gaba.

Zaben Ekiti: Ana wasu gyare-gyare a Jam’iyyar APC domin a kai ga nasara Inji Ogundana

Ayodele Fayose ya kifar da Gwamnatin APC a 2014

Jaridar Daily Trust ta rahoto mana Birgediya Janar Ebenezer Oguduna yana cewa Jam’iyyar APC ta na kokarin ganin yadda za tayi wajen lashe zaben Gwamnan Jihar Ekiti da aka shirya za ayi a tsakiyar watan Yuli mai zuwa.

KU KARANTA: Wasu 'Yan Jam'iyyar APC sun koma PDP a Jihar Abia

Janar Ebenezer Oguduna yana cikin jiga-jigan Jam’iyyar APC da ke adawa a Jihar yace Jam’iyyar za ta shirya wajen ganin ta karbe Jihar Ekiti daga hannun PDP inda yanzu Ayodele Fayose ya ke shirin barin kujera bayan yayi wa’adi 2.

Tsohon Sojan yana sa rai Jam’iyyar ta lashe zaben Gwamnan Jihar da za ayi sannan kuma da sauran zabukan da za su biyo baya a kasar. Jam’iyyar na kokarin yin duk abin da za ta iya domin ganin ta kai ga nasara a Jihar Ekiti bana.

A kwanan nan an rahoto cewa Wole Soyinka yayi kira ga Matasan kasar nan su shiga harkar siyasa a rika damawa da su lokacin da yake jawabi a wata Jami’a a Jihar Ondo a makon jiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel