Nigerian news All categories All tags
Wani 'Dan Shekara 40 ya Kashe kansa a jihar Ebonyi

Wani 'Dan Shekara 40 ya Kashe kansa a jihar Ebonyi

Wani haifaffen jihar Enugu mai shekaru 40 a duniya, Emmanuel Igwe da ya shahara da sunan Ezuego, ya kashe kansa a jihar Ebonyi ba tare da sanin dalilin sa ba.

Marigayi Igwe kafin cikawar sa ma'aikacin wani gidan abinci ne dake reshen Ishieke na jami'ar jihar Ebonyi a birnin Abakaliki.

Wani 'Dan Shekara 40 ya Kashe kansa a jihar Ebonyi

Wani 'Dan Shekara 40 ya Kashe kansa a jihar Ebonyi

Rahotanni sun bayyana cewa an tsinci gawar sa ne tana reto jikin wata bishiya dake bayan Cocin Pentecostal akan babbar hanyar Highlander tun da safiyar ranar Alhamis din da ta gabata.

Legit.ng ta fahimci cewa, marigayi Igwe ya mutu ya bar matar sa guda da 'ya'ya da dama.

KARANTA KUMA: Manyan Dakarun Sojin Sama 146 sun kammala nazarin Kula da Jagoranci a jihar Kaduna

Wata diyar sa mace, Uzoamaka yayin ganawa da manema labarai cikin hawaye ta bayyana cewa, mahaifin su dai ya fita kamar yadda ya saba a kullum inda bayan wani tsawon lokaci sai ya kirayi mahaifiyar su ta wayar salula ya umarce ta akan kula da su.

A cewar ta, mahaifin su bai ko tsaya amsa tambayoyin mahaifiyar su ba yayin da ya katse kiran inda daga bisani sai mummunan rahoto suka samu na mutuwar sa.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wani sabon rikici ya salwantar da rayuka 10 a jihar Abia dake kudancin Kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel