Nigerian news All categories All tags
Abdul'aziz Yari: Gwamnoni basu da iko akan jami'an tsaro

Abdul'aziz Yari: Gwamnoni basu da iko akan jami'an tsaro

- Gwamnan Zamfara, Abdul'aziz Yari yace, gwamnonin jihohi baza su iya daukar nauyin jami'an tsaro ba a yankunan su, tunda ba sune suke da iko dasu ba

Abdul'aziz Yari: Gwamnoni basu da iko akan jami'an tsaro

Abdul'aziz Yari: Gwamnoni basu da iko akan jami'an tsaro

Gwamnan Zamfara, Abdul'aziz Yari yace, gwamnonin jihohi baza su iya daukar nauyin jami'an tsaro ba a yankunan su, tunda ba sune suke da iko dasu ba. Yari, wanda jihar sa take fama da yawan kashe-kashe na 'yan ta'adda, ya shaidawa manema labarai a birnin Abuja a karshen wani taro da aka gudanar na Gwamnoni, inda yake cewa gwamnoni suna iya bakin kokarin su ta hanyar yin aiki da gwamnatin tarayya, domin ganin an magance matsalar tsaro a kasar nan.

DUBA WANNAN: Hukumar zabe tayi alkawarin tabbatar da gaskiya a kiranyen da ake yiwa Dino Melaye

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewar wannan shine karo na uku da gwamnonin suka zauna a wannan shekarar, a zaman anyi kira don magance matsalolin da gwamnoni ke fuskanta a jihohin su tsakanin su da gwamnatin tarayya.

'Ba mu da iko a kan sojoji ko' yan sanda ko wasu jami'an tsaro amma abin da za mu iya yi shi ne mu zauna tare da jami'an tsaro a jihohinmu don tallafa musu wurin tafiyar da aikin su.

'' Game da kayan aiki, muna yin iya bakin kokarin mu, kuma za mu ci gaba da tallafawa gwamnatin tarayya a wannan batun.

Gwamnan yace matsalar tsaro ba wai iya Najeriya bace kawai ke fama da matsalar tsaro kowacce kasa a duniyar nan ana fama da matsalar tsaro.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel