Nigerian news All categories All tags
Rikicin Iyaka: Mutane 10 sun rasa rayukan su a jihar Abia

Rikicin Iyaka: Mutane 10 sun rasa rayukan su a jihar Abia

A ranar Juma'ar da ta gabata ne wasu 'yan ta'adda da ake zargin sun fito ne daga garin Utuma na karamar hukumar Biase ta jihar Cross River, sun kai farmaki kan al'ummar Isu dake karamar hukumar Arochukwu ta jihar Abia inda suka salwantar da rayukan mutane goma.

An kone gidaje da dama a wannan harin da ya afku inda a baya dai dama al'ummar Isu dake karamar hukumar ta Arochukwu a jihar Abia sun taba gwabzawa da al'ummar Utuma ta jihar Cross River a wani rikici na kan iyaka.

Rikicin Iyaka: Mutane 10 sun rasa rayukan su a jihar Abia

Rikicin Iyaka: Mutane 10 sun rasa rayukan su a jihar Abia

Rahotanni dai sun bayyana cewa, sakamakon artabun da ya afku a ranar Juma'ar da ta gabata ya salwantar da dukiya gami da mahallai da aka kone wanda a yanzu kowa ya yi aron kafar Kare.

Legit.ng ta fahimci cewa, jami'an tsaro na 'yan sanda da dakarun sojin kasa sun kai ziyara wannan yanki sai dai kafin zuwan su tuni an ci kasuwa an watse, domin kuwa sai ragowar hayakin wuta suka riska da ta salwantar da tarin dukiya mai dumbin yawa.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya yi Fashin Baƙi kan wasiƙar Obasanjo

A yayin haka kuma wani shugaba kuma babban jigo na siyasa a yankin, Cif David Ogaba Onuoha, ya yi kaico tare da Allah wadai da wannan hari na zalunci da ya afku kan al'ummar Isu.

Cif Onuoha ya kirayi hukumar kula da iyaka da gaggawa akan ta shiga cikin lamari domin fayyace iyakar kowa da hakan zai taimaka wajen kiyaye afkuwar makamancin wannan ta'addanci a karo na gaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel