Nigerian news All categories All tags
A bisa dukkan alamu dai Dino Melaye zai samu nasara a kiranyen da ake yi masa

A bisa dukkan alamu dai Dino Melaye zai samu nasara a kiranyen da ake yi masa

- A yau ne aka fara gabatar da kiranye ga Sanatan jihar Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye, sai dai kuma ba a samu halartar mutane da yawa ba. Inda a wurin zabe na Lokoja Club 016 dake Lokoja, a cikin mutum 875 da suka saka hannu domin dawo dashi gida mutum biyu ne kawai suka halarci wurin zaben

A bisa dukkan alamu dai Dino Melaye zai samu nasara a kiranyen da ake yi masa

A bisa dukkan alamu dai Dino Melaye zai samu nasara a kiranyen da ake yi masa

A yau ne aka fara gabatar da kiranye ga Sanatan jihar Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye, sai dai kuma ba a samu halartar mutane da yawa ba. Inda a wurin zabe na Lokoja Club 016 dake Lokoja, a cikin mutum 875 da suka saka hannu domin dawo dashi gida mutum biyu ne kawai suka halarci wurin zaben.

DUBA WANNAN: Oyegun ya janye bayan da APC ta fitar da ranakun taron jam'iyya

Hakazalika, da karfe 11 na safiyar yau a wurin zabe na Ukwo Okoriko 003 dake karamar hukumar Koton Karfe, a cikin mutum 440 mutum 18 ne kawai suka halarci wurin.

Sai kuma wurin zabe na Ohagabi Voltage 003 karamar hukumar Koton Karfe da karfe 11:33 na safiyar yau an samu mutum 43 daga cikin 500 da suka saka hannun kiranyen ga sanatan.

A rahoton da muka samu da karfe 12 na rana, a wurin zabe na Oworo 012 dake Lokoja, mutum 40 ne kawai suka fita a cikin mutum 500

Da misalin 12:27 na rana, a wurin zabe na Felele kuwa a cikin mutane 815 da suka saka hannu domin kiranye ga sanatan ko mutum daya bai halarci wurin zaben ba a yau.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel