Nigerian news All categories All tags
Oyegun ya janye bayan da APC ta fitar da ranakun taron jam'iyya

Oyegun ya janye bayan da APC ta fitar da ranakun taron jam'iyya

- Jam'iyyar APC ta sanar da sabon ranar da zata gabatar da zaman ta na majalisa na wannan shekara daga matakin kananan hukumomi da kuma jihohi, kamar yanda majiyar mu ta jiyo jiya cewa shugaban jam'iyyar na kasa Cif John Odigie Oyegun, ya gama shirin fitowa shugaban jam'iyyar a karo na biyu. Amma duk da haka wasu na ganin cewar shawarar fitowa shugaban jam'iyyar na Oyegun yana da dangantaka da ziyarar da ya kai fadar shugaban kasa ranar Alhamis dinnan da daddare

Oyegun ya janye bayan da APC ta fitar da ranakun taron jam'iyya

Oyegun ya janye bayan da APC ta fitar da ranakun taron jam'iyya

Jam'iyyar APC ta sanar da sabon ranar da zata gabatar da zaman ta na majalisa na wannan shekara daga matakin kananan hukumomi da kuma jihohi, kamar yanda majiyar mu ta jiyo jiya cewa shugaban jam'iyyar na kasa Cif John Odigie Oyegun, ya gama shirin fitowa shugaban jam'iyyar a karo na biyu. Amma duk da haka wasu na ganin cewar shawarar fitowa shugaban jam'iyyar na Oyegun yana da dangantaka da ziyarar da ya kai fadar shugaban kasa ranar Alhamis dinnan da daddare.

DUBA WANNAN: Ashe bayan 'yan matan Chibok dana Dapchi 'yan Boko Haram sun sace mutane da yawa a jihar Borno

Amma kuma ranar Talatar nan, ya bayyana cewa tsayar da tsohon gwamna Adams Oshiomhole da shugabannin jam'iyyar na kudancin kasar suka yi bai kamata ba, Cif Oyegun, wanda yayi magana da manema labarai a babbar sakatariyar jam'iyyar dake birnin tarayya Abuja, yace dole za'a gudanar da zaben ne a wani wuri daban ba wai a gidan gwamnati ba. Sannan kuma yace akan maganar fitowar shi takara, da farko yana so ya fara sannin yaushe jam'iyyar zata gabatar da shirye-shiryen ta, sannan kuma na san lokacin da zan saya katin fitowa takara, to a lokacin ne zan yanke hukunci, sannan kuma a lokacin ne zan sanar daku manufa ta.

A jiya ne jam'iyyar ta sanar da sabon ranar da zata yi taron, sanarwar ta fito daga bakin sakataren jam'iyyar na kasa, Malam Bolaji Abdullahi, inda yace sun yanke ranar 5 ga watan Mayun wannan shekarar domin gabatar dana kauyuka, sai kuma 12 ga watan za'ayi na kananan hukumomi, sannan ranar 19 ga wata za'ayi na jihohi.

Abdullahi yace za'a sanar da ranar da za'ayi taron na kasa baki daya a watan Yuni.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel