Nigerian news All categories All tags
Ashe bayan 'yan matan Chibok dana Dapchi 'yan Boko Haram sun sace mutane da yawa a jihar Borno

Ashe bayan 'yan matan Chibok dana Dapchi 'yan Boko Haram sun sace mutane da yawa a jihar Borno

- Rahotanni daga PAGED Initiative, wata kungiya mai zaman kanta ta kasa tace akwai mutane da yawan gaske da suke zaune a sansanin 'yan gudun hijira wanda gwamnati batan san da su ba, sannan a wani rahoto da kungiyar ta fitar ta nuna cewar akwai mutane da yawa wanda suke zaune a sansanin 'yan gudun hijiran wanda 'yan kungiyar Boko Haram suka sace musu iyalan su wanda har yanzu ba a san inda suke ba a jihar ta Borno

Ashe bayan 'yan matan Chibok dana Dapchi 'yan Boko Haram sun sace mutane da yawa a jihar Borno

Ashe bayan 'yan matan Chibok dana Dapchi 'yan Boko Haram sun sace mutane da yawa a jihar Borno

Rahotanni daga PAGED Initiative, wata kungiya mai zaman kanta ta kasa tace akwai mutane da yawan gaske da suke zaune a sansanin 'yan gudun hijira wanda gwamnati batan san da su ba, sannan a wani rahoto da kungiyar ta fitar ta nuna cewar akwai mutane da yawa wanda suke zaune a sansanin 'yan gudun hijiran wanda 'yan kungiyar Boko Haram suka sace musu iyalan su wanda har yanzu ba a san inda suke ba a jihar ta Borno.

DUBA WANNAN: An samu Man Fetur da Iskar Gas mai yawa a Arewacin Najeriya

Rifkatu Bitrus 'yar asalin karamar hukumar Bama ce, wacce a yanzu haka take zaune a sansanin 'yan gudun hijira dake Wulari. Ta ce 'yan ta'addar sun kashe 'yan uwanta maza sannan suka tafi da matayensu su tara, kuma har yau babu labarin su.

Bitrus Yakubu, wanda ya rasa kawunsa da kakansa a lokacin da 'yan ta'addar suka kai hari garin su, yace tunda 'yan ta'addar suka tafi da kanwarsa har yau bai kara saka ta a idon sa ba.

Haka shima Malam Ibrahim Sama'ila ya bada nashi labarin yace "An tilasta wa kanwata ta auri wani dan Boko Haram, inda daga baya ta mutu a Ngoshe a lokacin da ta zo haihuwa a cikin 'yan ta'addar. Sannan kuma na rasa Kawuna da kuma wata 'yar uwartawa a lokacin da aka kawo hari Sabon Gari."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel