Nigerian news All categories All tags
Shugaba Buhari ya yi Fashin Baƙi kan wasiƙar Obasanjo

Shugaba Buhari ya yi Fashin Baƙi kan wasiƙar Obasanjo

Daga karshe dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya furuci akan budaddiyar wasikar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, wadda take caccakar gwamnatin sa da kuma gargadin sa kan sake tsayawa takarar shugabancin kasar nan a zaben 2019.

A wasika mai tsayin shafi 13 da tsohon shugaban kasar ya rubuta a watan Janairun da ya gabata, mun samu rahoton cewa shugaba Buhari ya gargadin dukkanin hadiman sa akan mayar da martani ga tsohon shugaba Obasanjo.

Sai dai a jawaban shugaba Buhari na ranar Alhamis din da ta gabata yayin wata liyafar karamci da aka shirya ma sa sakamakon ziyarar aiki ta yini biyu da ya kai jihar Bauchi ya bayyana cewa, tun da fari ya dakatar da ministan labarai Lai Muhammad, akan mayar da martani wanda daga bisani kuma yayi na'am da bukatar sa.

Shugaba Buhari ya yi Fashin Baƙi kan wasiƙar Obasanjo

Shugaba Buhari ya yi Fashin Baƙi kan wasiƙar Obasanjo

A kalaman shugaba Buhari, "A yau ina so in tunatar da ku abinda Lai Muhammad ya yi yayin da wasika mai caccakar gazawar gwamnatin mu ta bayyana. Lai Muhammad ya lashi takobbi akan mayar da martani amma na dakatar da shi."

"Dalilin farko na dakatar da shi shine; ta fuskar shekaru da ni da Lai Muhammad duk kasa muke akan wanda ya rubuta wasikar. Dalili na biyu kuma shine Lai Muhammad da marubucin wasikar duka sun fito ne daga mahaifa daya ta jihar Ogun."

"A yayin da Ministan ya sake dawo, sai nace har yanzu bai hakura ba ya kuma ce ai ba zai iya jurewa ba kuma yana rokon na ba shi dama ya bayyana abin da ke zuciyar sa."

KARANTA KUMA: Tsananin Kyawun Matar sa: Ya nemi Kotu ta raba auren su

"Hakan kuwa aka yi amma tare da gargadin sa akan kar ya sake ya kama suna face tunatar da 'yan Najeriya abinda muka riska yayin karbar mulki da kuma rawar da muka taka kawowa yanzu."

A yayin haka Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaba Buhari ya yabawa kwazon Ministan dangane da dattakon da ya aiwatar wajen mayar da martanin wasikar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel