Wani babban Fasto ya shawarci Kiristoci su dena aibanta shugaba Buhari

Wani babban Fasto ya shawarci Kiristoci su dena aibanta shugaba Buhari

- Yace shugabanni suna gazawa ne a lokacin da al'umma suka gaza dayi musu addu'a

- Ya kamata mudinga yiwa wannan kasa addu'a saboda mutane marasa laifi da ake kashewa

- Ya kamata shugaban kasa yayi duk wani abinda zai iya don kawo karshen wannan kashe kashe

Shugaban cocin Christ Apostolic CAC, na fadin duniya, Abraham Akinosun ya roki majami'u dasu daina kokawa suci gaba da yiwa shugaban kasa Muhammad Buhari addu'a a kan wannan kalubale da yake fuskanta a kasar nan.

Akinosun yayi wannan rokon a ranar karshe ta azumin makwanni 7 da addu'a daya gudana a dutsen Ikoyi kauyen Ero-Omo dake Osun a safiyar Asabar.

Wani babban Fasto ya shawarci Kiristoci su dena aibanta shugaba Buhari

Wani babban Fasto ya shawarci Kiristoci su dena aibanta shugaba Buhari

KU KARANTA: Wata kasar Afirka ta halasta amfani ta ganyen wiwi

Yace "ya zama dole yan Najeriya su tuba".

Akimosun tsohon ciyaman na CAC, yace Allah ne kadai zai fitar da Najeriya daga cikin yanayin.

Yace "shugabanni suna gazawa ne a lokacin da al'umma suka gaza dayi musu addu'a, adadin tsinuwar ku ga shugabanni adadin tabarbarewar lamuran ku"

"Idan munayi wa shugabannin mu addu'a Allah zai shiga lamarin komai ya tafi yanda ya kamata. Bamu yanke kauna ga nageriya ba.

Ya kamata mu dinga yiwa kasar nan addu'a ko saboda mutane marasa laifi da ake kashewa.

"Ya zama dole shugaban kasa yayi kokari wajen kawo karshen kashe kashe da akeyi."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel