Nigerian news All categories All tags
2019: Buhari ya bayyana dalilin da zai sanya ya sake samun nasara

2019: Buhari ya bayyana dalilin da zai sanya ya sake samun nasara

A ranar Alhamis din da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kudirin sa karara na sake neman kujerar sa a karo na biyu, inda ya tunatar da cewar ya nemi wannan kujera sau da dama a baya amma bai taki nasara ba.

Shugaban kasar ya yi wannan batu ne a farfajiyar wasanni ta Abubakar Tafawa Balewa dake jihar Bauchi a yayin ziyarar aiki ta kwanaki biyu da kai jihar.

Legit.ng ta fahimci cewa, shugaba Buhari ya bayyana wannan kudiri ga shugabannin jam'iyyar sa ta APC kafin ya kama hanyar sa ta halartar taron Commonweath da aka gudanar a birnin Landa na kasar Ingila.

Shugaba Buhari yayin ziyarar aiki a jihar Bauchi

Shugaba Buhari yayin ziyarar aiki a jihar Bauchi

Wannan sanarwa ta bayyana kudirin shugaban kasa ta zo ne da sanadin gwamnan jihar Filato; Simon Lalong, na jihar Kaduna; Nasir El-Rufa'i da kuma hadiman sa.

A yayin tabbatar da dalilin wannan kudiri a jihar ta Bauchi, shugaba Buhari ya bayyana cewa duk da kasancewa ya nemi wannan kujera har a karo uku amma bai samu nasara ba sai a karo na hudu, ya na da tabbacin samun nasara a zaben 2019 domin kuwa al'ummar kasar nan ba su da haufi a kansa.

KARANTA KUMA: Kauracewa Kwanciyar Iyali: Wata Mata ta roki Kotu ta raba auren ta da Mijin ta

Da wannan yakini ne shugaban kasar yake jinjina tare da godiya ga al'ummar kasar nan dangane da irin soyayya da kuma goyon baya maras yankewa da suke ci gaba da nuna wa a gare shi.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, ba ya da halin son zuciya na almundahana da wawason dukiyar kasa kamar yadda wasu shugabannin kasar nan da suka shude suka aikata, inda ya bayar da misalin yadda ya jagoranci cibiyar PTF (Petroleum Trust Fund) kuma ya rike ta da amana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel