Nigerian news All categories All tags
"Mulkin Buhari ne ya sanya na sayar da diya ta"

"Mulkin Buhari ne ya sanya na sayar da diya ta"

Wani magidanci mai shekaru 35 a duniya mai suna Nkemakolam Ugorji da matar sa mai suna Happiness sun ansa cewa tsananin yunwa da talauci irin na mulkin shugaba Buhari shine ya tilasta su suka sayar da diyar su mai kwanaki 2 kacal a duniya.

Ma'auratan dai sun bayyana cewa kawo yanzu shekarun su bakwai da aure kuma yanzu haka suna da 'ya'ya hudu wadanda da kyar suke ciyar da su hakan ne ma yanzu da suka haifi na biyar din sai suka yanke shawarar sayar da ita.

"Mulkin Buhari ne ya sanya na sayar da diya ta"

"Mulkin Buhari ne ya sanya na sayar da diya ta"

KU KARANTA: Ranar Talata ta zama ranar hutu

Legit.ng ta samu cewa mahaifiyar jaririyar ta shaidawa majiyar ta mu cewa malamar jinyar da ta karfi haihuwar ta ita ce ta hada ta da wadda ta sayi jaririyar akan kudi Naira dubu dari 3.

A wani labarin kuma, Majalisar zartaswar Najeriya ta ayyana amincewar ta da tayi da kashe zunzurutun kudi har Naira biliyan 10.7 domin kafa kamfanonin sarrafa shinkafa guda 19 a cikin kuma jahohi 10 a fadin kasar nan.

Sanarwar hakan kamar yadda muka samu ta fito ne daga bakin karamin ministan harkokin noma Mista Heineken Lokpobiri a lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadar shugaban kasa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel