Nigerian news All categories All tags
Dalilin da yasa gwamnoni basu iya samar da ingantaccen tsaro a jihohinsu - Yari

Dalilin da yasa gwamnoni basu iya samar da ingantaccen tsaro a jihohinsu - Yari

- Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara yace gwamonin jihohi baza su iya samar ta cikaken tsaro a jihohinsu ba saboda basu da iko da hukumomin tsaro na kasa

- Yayi bayyani cewa sojoji da Yan sanda da sauran jami'an tsaro duk suna karkashin gwamnatin tarayya ne

- Yace abinda gwamnonin jihohi kawai zasu iya taimakawa dashi shine taimakawa jami'an tsaron shine taimako na fanin tafiye-tafiye da kulawa da ababen hawan wanda kuma sunayi

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), Gwamna Abdulaziz yari na jihar Zamfara yace gwamnonin jihohi baza su iya samar da ingantaccen tsaro a johohinsu ba saboda basu da ikon a kan jami'an tsaron kamar yadda kamfanin dillanci labarai (NAN) ta ruwaito.

Yari ya shaidawa manema labarai a babban birnin tarayya Abuja bayan wani taron da gwamnonin sukayi a ranar Alhamis, 27 ga watan Afrilu, inda ya kara da cewa gwamonin suna aiki tare da gwamnatin tarayya don ganin su magance matsalar tsaro da ke adabar wasu sassan kasar nan

Dalilin da yasa gwamnoni basu iya samar da ingantaccen tsaro a jihohinsu - Yari

Dalilin da yasa gwamnoni basu iya samar da ingantaccen tsaro a jihohinsu - Yari

Legit.ng ta gano cewa wannan taron da gwamnonin sukayi shine irinsa karo na uku da akayi a wannan shekarar kuma an kira taron ne saboda a lalubo hanyoyin da za'a bi don magance matsalar rashin tsaro.

KU KARANTA: Dalilin da yasa ban amsa kiran Majalisar Dattawa ba - Sufeta Idris

Yace: "Bamu da ikon akan hukumomin tsaro kamar Sojoji da Yan sanda da ma sauran hukumomin tsaron, abinda kawai zamu iya yi shine mu zaune tare dasu don mu san yadda zamu taimaka musu.

"A fanin tsare-tsare da samar da ababen hawa, muna yin iya kokarinmu don ganin mu taimakawa gwamnatin tarayya."

Gwamna Yari kuma ya shaidawa manema labaran cewa matsalar rashin tsaron ya zama ruwan dare a duniya domin gwamnatocin sauran kasashen duniya suma suna fama da shi.

Ya kuma ce dama gwamnatinsu ta gaji matsalar rashin tsaron ne daga gwamnatin da ta shude amma suna iya kokarinsu na ganin sun magance matsalar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel