Nigerian news All categories All tags
Sanata Omo Agege ya kai majalisa da AGF kara kotu

Sanata Omo Agege ya kai majalisa da AGF kara kotu

- Kotun tarayya ta sanya ranar 30 ga watan Afirilu, ranar da zata saurari karar da Sanata Ovie Omo-Agege ya kai shugaban majalisa da shugaban ma’aikata na tarayya ya shigar a gabanta

- Omo-Agege wanda ke wakiltar mazabar jihar Delta ta tsakiya, ya shigar da kara don ya kalubalanci dakatarwar da majalisar tayi masa daga majalisar

- Alkalin Justice Nnamdi Dimgba, ya sanya ranar sauraren kara ne bayan yaki amincewa da bata lokaci wurin shari’ar

Kotun tarayya ta sanya ranar 30 ga watan Afirilu, ranr da zata saurari karar da Sanata Ovie Omo-Agege ya kai shugaban majalisa da shugaban ma’aikata na tarayya ya shigar a gabanta, a ranar 27 ga watan Afirilu na shekarar 2018, a birnin tarayya.

Omo-Agege wanda ke wakiltar mazabar jihar Delta ta tsakiya, ya shigar da kara don ya kalubalanci dakatarwar da majalisar tayi masa daga majalisar.

Alkalin Justice Nnamdi Dimgba, ya sanya ranar sauraren kara ne bayan yaki amincewa da bata lokaci wurin shari’ar.

Sanata Omo Agege ya kai majalisa da AGF kara kotu

Sanata Omo Agege ya kai majalisa da AGF kara kotu

Lauyan da majalisar ta hada da Sanata Omo-Agege, Mr. Alex Izinyon (SAN) ya bukaci kotun da bukatarsa ta bawa majalisar lokaci kafin a saurari kara, amma kotun bata amince ba.

KU ARANTA KUMA: Dudda bashin albashi da ma’aikata ke bi, amma bai hana gwamnonin APC hada N6bn don zagayen jam’iyyar ba

Alkalin Justice Dimgba ya bukaci Izinyon da ya sanar da majalisar da kuma shugaban majalisar, sannan ya umurceshi da ya bayyana masa dalilin da yasa majalisar bazata amince da bukatar Sanatan ba ta bayyana a gaban shari’a.

Kotun ta bawa Lauyan kwanaki bakwai ya gabatar da wadanda kotun ke bukata, kuma zata gaggauta shari’ar, sakamakon haka ta daga sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Afirilu, lokacin da zata saurari karar har zuwa karshen shari’ar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=e

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel