Nigerian news All categories All tags
Almundahanan N5.7bn: Kotu ta baiwa Shema beli

Almundahanan N5.7bn: Kotu ta baiwa Shema beli

Wata babban kotuna tarayyan da ke zaune a jihar Katsina a yau Juma’a ta baiwa tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema, beli.

An gurfanar da tsohon gwamnan a gaba kotu kan laifuka 26 kan almundahanan kudade kimanin N5.7bn na shirin Sure-P da ake zargin ya wawusa.

Lauyan Shema, Mr Joseph Daudu, ya bukaci kotun ta basa belin bisa ga kundin tsarin mulkin Najeriya.

Ya jawo hankalin kotun cewa kasancewan Shema tsohon gwamna, ba zai saba ka’idojin beli ba idan aka basa.

Almundahanan N5.7bn: Kotu ta baiwa Shema beli

Almundahanan N5.7bn: Kotu ta baiwa Shema beli

Amma lauyan gwamnati, Dr J.O Olatoke, SAN, yace bai amince ba da wannan bukata be saboda an samu rahotannin leken asiri cewa idan har aka sake aka basa beli, ba zai cika ka’idojin belin ba.

Ya ce tuni Shema ya kai wata kara babban kotun tarayya da ke Abuja domin bukatar aka basa katin fasfot na fita kasar waje.

KU KARANTA: Hadin kan Najeriya ne babban hammi na – Shugaba Buhari yayinda ya karbi bakuncin shugabannin Tijjaniyya

Amma a shari’ar alkalin kotun, Justice Babagana Ashigar, ya baiwa Ibrahim Shehu Shema belin; kuma ya daga zaman zuwan ranan 12 ga watan Yuni, 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel