Nigerian news All categories All tags
Hadin kan Najeriya ne babban hammi na – Shugaba Buhari yayinda ya karbi bakuncin shugabannin Tijjaniyya

Hadin kan Najeriya ne babban hammi na – Shugaba Buhari yayinda ya karbi bakuncin shugabannin Tijjaniyya

A yau Juma’a, 27 ga watan Afrilu 2018, shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaban darikar Tijjaniyya a fadar shugaban kasa da ke Aso Villa, babban birnin tarayya Abuja.

Shugabannin darikar karkashin jagorancin Khalifan Shayhk Ibrahim Inyass, Sheikh Muhammadu Mahi Ibrahim Inyass, sun kawo ziyara na musamman ne bayan sun kamala taron Maulidin mahaifinsa da akayi a Abuja da Kaduna a kwanakin baya.

Shugaba Buhari ya bayyana musu cewa zai cigaba da iyakan kokarinsa wajen tabbatar da hadin kan yan Najeriya.

Shugaban kasan ya yabi kungiyoyin addinin da gudanar da taron Maulidin cikin zaman lafiya da lumana; kana ya yi kira ga suyi amfani da irin wannan dama wajen hadin kai da zaman lafiyan addinai a Najeriya.

Hadin kan Najeriya ne babban hammi na – Shugaba Buhari yayinda ya karbi bakuncin shugabannin Tijjaniyya

Hadin kan Najeriya ne babban hammi na – Shugaba Buhari yayinda ya karbi bakuncin shugabannin Tijjaniyya

Yayinda yake nanata maganan da yayi a fadar sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu, a ziyarar da ya kai jiya inda kaa basa kyautan Al-Kur’ani mai girma, shugaba BUhari y ace kyautan Al-Kur’ani shine kyauta mafi girma da za’a iya baiwa mutum.

KU KARANTA: Dan Najeriya ya ci gagarumar kyauta a musabaka a kasar Iran

A jawabin Sheikh Muhammadu Mahi Ibrahim Inyass, ya bayyanawa shugaba Muhammadu Buhari cewa mambobin darikar za su cigaba da goya masa baya da kuma aikin da yakewa yan Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel