Dudda bashin albashi da ma’aikata ke bi, amma bai hana gwamnonin APC hada N6bn don zagayen jam’iyyar ba

Dudda bashin albashi da ma’aikata ke bi, amma bai hana gwamnonin APC hada N6bn don zagayen jam’iyyar ba

- Dudda wahalhalu da ma’aikata ke fuskanta da ‘yan fansho na watanni ba kudi, amma gwamnoni 24 na karkashin jam’iyyar APC sun shirya bayar da gudunmuwar N6bn na zagayen jam’iyya

- Gwamnonin ana tsammanin zasu bayar da kudaden ne daga asusun jihohin nasu wanda kowane a cikinsu zai bayar da N250m

Dudda wahalhalu da ma’aikata ke fuskanta da ‘yan fansho na watanni ba kudi, amma gwamnoni 24 na karkashin jam’iyyar APC sun shirya bayar da gudunmuwar N6bn na zagayen jam’iyya, kamar yadda majiyarmu ta Premium Times ta samu labari.

Gwamnonin ana tsammanin zasu bayar da kudaden ne daga asusun jihohin nasu wanda kowane a cikinsu zai bayar da N250m a matsayin tasa gudunmuwar. Bayan daga watan Fabrairu na wannan shekarar 23 cikin gwamnonin suna da matsalar albashi ko kudin fansho kuma duka, banda jihar Legas.

Dudda bashin albashi da ma’aikata ke bi, amma bai hana gwamnonin APC hada N6bn don zagayen jam’iyyar ba

Dudda bashin albashi da ma’aikata ke bi, amma bai hana gwamnonin APC hada N6bn don zagayen jam’iyyar ba

Gwamnonin sune Bindo Jibrilla na jihar Adamawa, Mohammed Abubakar na jihar Bauchi, Samuel Ortom na jihar Binuwai, Kashim Shettima na jihar Borno, Godwin Obaseki na jihar Edo, Rochas Okorocha na jihar Imo, Abubakar Badaru na jihar Jiagawa, Nasir El-Rufa’I na jihar Kaduna, Aminu Bello Masari na jihar Katsina, Abubakar Bagudu na jihar Kebbi, da kuma Yahaya Bello na jihar Kogi.

KU KARANTA KUMA: Najeriya zatayi taron kasuwanci a kasar Sin

Sauran sune Abdulfatah Ahmed na jihar Kwara, Akinwunmi Ambode na jihar Legas, Umaru Tanko Almakura na jihar Nasarawa, Abubakar Bello na jihar Niger, Ibikunle Amosun na jihar Ogun, Oluwarotimi Aregbesola na jihar Osun, Abiola Ajimobi na jihar Oyo, Simon Lalong na jihar Filato, Aminu Tambuwal na jihar Sokoto, Ibrahim Geidam na jihar Yobe, da Abdulaziz Yari na jihar Zamfara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=e

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel