Nigerian news All categories All tags
Najeriya zatayi taron kasuwanci a kasar Sin

Najeriya zatayi taron kasuwanci a kasar Sin

- Najeriya zata hada taron kasuwanci a garin Shanghai, dake kasar Sin a ranar 20 ga watan Afirilu na shekarar 2018

- Taron wanda jami'an gwamnatin Najeriya dake aiki a can zasu kaddamar, za'ayi ne don kara dankon zumci ta fannin kasuwanci tsakanin Najeriya da kasar ta Sin

- Taron wanda za'a gudanar a garin Shanghai game da kasuwanci tsakanin Najeriya da Sin na fannin kasuwancin da ayyukan cigaba da da kuma zuba hannayen jari da kuma fannin noma a kasashen biyu

Manyan jami'an Najeriya dake kasar Sin zasu kaddamar da taron kasuwanci a garin Shanghai tsakanin Najeriya da Sin, don kara karfin kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Shugaban jami'an Anderson Madubike ya bayyana a wani labari da jaridar Daily Trust ta bayar cewa za'a gudanar da taron ne a garin Sin don kara samun cigaba ta fannin ayyukan cigaba da zuba hannayen jari da kuma bunkasa noma tsakanin kasashen biyu.

Najeriya zatayi taron kasuwanci a kasar Sin

Najeriya zatayi taron kasuwanci a kasar Sin

Madubike ya jinjinawa 'yan Najeriya dake zama a kasar ta Sin, saboda yanda suka jajirce suka koyi yaren kasar don yin karatu a kasar ko kuma aiwatar da kasuwanci tsakaninsu da mutanen kasar.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari zai tafi kasar Amurka a ranar Asabar zai gana da Trump da sauransu

An kaddamar da kungiyar ne a shekarar 2008 tsakanin Najeriya da kasar Sin, don cigaban tattalin arziki da kuma kasuwanci tsakanin Najeriya da kasar ta Sin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=e

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel