Nigerian news All categories All tags
Rikita-rikita: An kama lauyan bogi a kotu yana kare mai laifi, an garkame shi

Rikita-rikita: An kama lauyan bogi a kotu yana kare mai laifi, an garkame shi

Bayan ya shafe shekaru uku yana tsula tsiyarsa, asirin wani lauyan bogi, Samson Obu, ta tonu a wata kotun majistare da ke zamanta a unguwar Ikorodu da ke jihar Legas.

Kotu da damke mutumin mai shekaru 43, mazaunin gida mai lamba 5 layin Imam a Owuta Ikorodu bayan wasu takwarorinsa lauyoyi sun bayyana shaku a kansa.

Kamar yadda Dansanda mai shigar da kara, Saja John Iberedem ya bayyana, wanda ake zargin ya bayyana a kotu ne don kare wani wanda ake tuhuma a ranar 5 ga watan Afrilu amma da ya tashi karanto wata sashi a doka, sai ya karanto ba dai-dai ba.

Rikita-rikita: An kama lauyan bogi a kotu yana kare mai laifi, an garkame shi

Rikita-rikita: An kama lauyan bogi a kotu yana kare mai laifi, an garkame shi

KU KARANTA: Toh fah: Majalisar Wakilai zata bada sammacin a kamo mata wasu mukarraban shugaba Buhari

Hakan ya sanya sauran lauyoyin suka fara samun shakku a kansa, ciki harda maitaimakin kungiyan lauyoyin najeriya Mr. Adetayo Ladega. Hakan yasa Mr. Ladega da sauran lauyoyin suka turke shi da tambayoyi kuma suka mika shi ga Yan sanda.

"Wanda ake zargin ya kwashe shekaru uku yana zuwa kotu yana kare mutane a matsayin lauya," inji Iberedem kuma ya kara da cewa laifin ya ci karo da sashi na 78 na kundin manyan laifuka na 2015 na jihar Legas.

Sai dai kuma Obu bai amince da zargin da ake masa ba.

Alkalin kotun, Cif Mrs. F.A. Azeez ta bayar da belinsa a kan kudi N250,000 tare da mutane biyu masu tsaya masa. Mutane biyun sai sun gabatar da takardan biyan haraji na shekaru uku kana kowanensu ya bayar da jinginar N25,000.

Alkalin ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Mayu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel