Nigerian news All categories All tags
Shugaba Buhari zai tafi kasar Amurka a ranar Asabar zai gana da Trump da sauransu

Shugaba Buhari zai tafi kasar Amurka a ranar Asabar zai gana da Trump da sauransu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja a ranar Asabar domin ziyarar aiki kasar Amurka, inda zai amsa gayyatar da shugaba Donald Trump yayi masa.

Maiba shugaban kasa shawara na musamman a shafukan zumunta, Mista Femi Adesina a wata sanarwa da yayi a Abuja a ranar Juma’a, yace Buhari zai gana da shugaba Trump da kuma cin wani kwarya kwaryan walima na aiki a ranar 30 ga watan Afrilu.

A cewar Adesina, zaa gudanar da ganawar ne domin tattaunawa kan yadda zaa karfafa dabarun cinikai tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Buhari zai tafi kasar Amurka a ranar Asabar zai gana da Trump da sauransu

Shugaba Buhari zai tafi kasar Amurka a ranar Asabar zai gana da Trump da sauransu

Ya ce hakazalika taron zai habbaka muhimman abubuwa kamar kawo gaban tattalin arziki, yaki da rashawa da sauran ababen dake barazana ga zaman lafiya da tsaro.

KU KARANTA KUMA: Yadda Gwamnonin APC suka kusa ba hammata iska a wurin taro

Yace kafin zuwan shugaban kasar, an rigada an shirya ganawa tsakanin manyan jami’an gwamnatin Najeriya da manyan kamfanonin Amurka ta fannin noma, jiragen sama da sufuri a ranakun 26 da 27 ga watan Afrilu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=e

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel