Nigerian news All categories All tags
Jami’an Yansanda sun damko wuyar wani Matashi da ya yi ma matar kawunsa fyade

Jami’an Yansanda sun damko wuyar wani Matashi da ya yi ma matar kawunsa fyade

Rundunar Yansandan jihar Kano ta yi caraf da wani matashi mai suna Saifullahi Haruna bayan samun rahoton ya yi ma matar kawunsa fyade, kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Yansandan jihar sun gurfanar da matashin gaban wata Kotun majistri dake zamanta a majalisar Audu Bako, inda ya amsa laifinsa bayan Yarsanda mai kara Sufeta Mercy John ta karanto masa laifukansa.

KU KARANTA: Badakalar kudin makamai: Babbar Kotun tarayya ta kawo ma Dasuki cikas

“Saifullahi Haruna ya gayyaci abokinsa mai suna Sulaiman Auwal, inda suka fada ma matar Kawunsa da fyade, a garin Kabo na jihar Kano. Laifin da suka aikata ya saba ma sashi na 97 da 231 na kundin hukunta manyan laifuka.” Inji Sufeta Mercy

Jami’an Yansanda sun damko wuyar wani Matashi da ya yi ma matar kawunsa fyade

Wata Kotu

Bayan saurarn dukkanin bangarorin biyu, Alkali mai shari’a Salma Dan Baffa ta bada umarnin garkame mata Saifullahi da Sulaiman a gidan Kurkuku, daga nan ta dage sauraron karar har zuwa ranar 10 ga watan Mayu.

Awani labarin kuma, wani Malami mai suna Muhammad Suleiman, wanda ake tuhumarsa da laifin zakke ma dalibarsa mai shekaru 3, ya fada komar Yansandan jihar Kano, inda Malamin ya janyo ta cikin wani Aji dake makarantarsu a unguwar Rimin Gata, sai dai Malamin ya musanta aikata laifin.

Kwamishinan Yansandan jihar Kano ta bakin wakilinsa, Inspekta Pogu Lale ne ya gurfanar da wanda ake zargi a gaban Kotu, inda ya bayyana shi a matsayin matashi mai shekaru 26, dake zama a unguwar Rimin Gata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel