Nigerian news All categories All tags
Gwamnonin APC na kudu sun sha yabo bisa yadda suka goyi bayan tazarcen shugaba Buhari

Gwamnonin APC na kudu sun sha yabo bisa yadda suka goyi bayan tazarcen shugaba Buhari

- Gwamnoninn jam'iyyar APC na kudu sun sha yabo saboda goyon bayan tazarcen shugaba Muhammadu Buhari

- Shugabanin APC na yankin kudancin Najeriya sun bayyana farin cikinsu bisa matsayar gwamononin cikin wata sanarwa da suka fitar ranar Alhamis, 26 ga watan Afrilu

- Shugabanin jam'iyyar sunyi kira ga gwamnonin da mutanen yankin su cigaba da bawa shugaba Buhari goyon baya

Shugabanin jami'iyyar APC na kudu maso gabashin Najeriya sun yabawa gwamnonin jam'iyyar bisa yadda suka goyi bayan sake fitowa takarar shugaba Muhammadu Buhari karo na biyu.

Shugabanin sunyi wannan yabon ne a wata sanarwan bayan taro da suka fitar a garin Enugu bayan taron shugabanin jam'iyyar a ranar Alhamis, 26 ga watan Afrilu kamar yadda kamfanin dillancin labarai (NAN) ta ruwaito.

Gwamnonin APC na kudu sun sha yabo bisa yadda suka goyi bayan tazarcen shugaba Buhari

Gwamnonin APC na kudu sun sha yabo bisa yadda suka goyi bayan tazarcen shugaba Buhari

KU KARANTA: Akwai masu daukan nauyin makiyaya masu kai hari a Binuwai - Sojin Najeriya

Mataimakin Ciyaman na jami'iyyar APC reshen kudu maso gabas, Emma Eneukwu da sakataren yadda labarai na yankin, Hycienth Ngwu ne suka fitar da sanarwan da ke dauke da sa hannun shugabanin jam'iyyar.

Shugabanin sun kuma yi kira ga daukakin mutanen yankin su bawa shugaba Muhammadu Buhari goyon baya a yunkurinsa na zarcewa kan karagar mulkin Najeriya.

Wani sashi daga cikin sakon: "Muna kira da gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya da daukakin al'ummar yankin da su bawa shugaba Muhammadu Buhari goyon baya, saboda haka ne zai tabbatar da cewa dan kabilar Igbo ya zama shugaban kasa a 2023.

"Muna yabo ga shugaban kasan saboda irin ayyukan cigaba da yakeyi a yankin kudu maso gabas. Muna kuma godiya ga mambobin kwamitin gudanarwa na kasa da Ciyaman din jam'iyyar mu na jiha saboda cigaba da zaman lafiya da suka wanzar a jam'iyyar."

Taron ya samu hallarcin jiga-jigan jam'iyyar APC na yankin wanda suka hada da Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu da Minitan Kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel