Nigerian news All categories All tags
Majalisar Dattawa ta bayar da tabbacin zartar da wasu sabbin dokoki 2 a harkar Lafiya kafin 2019

Majalisar Dattawa ta bayar da tabbacin zartar da wasu sabbin dokoki 2 a harkar Lafiya kafin 2019

Majalisar dattawa ta bayar da tabbacin ta ga 'yan Najeriya na muhimmantuwa kan dokoki 2 a harkar kiwon lafiya da suka hadar da dokar hana fataucin muggan kwayoyi da kuma dokar ciwon hauka da za ta sanya cikin dokar kasa kafin 2019.

Majalisar Dattawa ta bayar da tabbacin zartar da wasu sabbin dokoki 2 a harkar Lafiya kafin 2019

Majalisar Dattawa ta bayar da tabbacin zartar da wasu sabbin dokoki 2 a harkar Lafiya kafin 2019

Babban hadimi na musamman ga shugaban majalisar akan harkokin kiwon lafiya, Mist Tony Isama, shine ya yi wannan karin haske na ranar Alhamis tare da bayar da tabbaci yayin ganawa da manema labarai a garin Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, majalisar tun a shekarar da ta gabata ta fara aiwatar da shirye-shirye akan dokokin domin kawo karshen shaye-shaye da ta'ammali da muggan kwayoyi musamman a tsakankanin matasan kasar nan.

Isama ya ke cewa, majalisar ta gudanar da wasu ganawa a karo daban-daban da masu ruwa da tsaki na bangaren addinai, kabilu da kuma kwararru kan harkokin kiwon lafiya domin samun bayanai da za su kasance a matsayin rataye na hujjoji da jagoranci.

KARANTA KUMA: Hukumar 'Yan Sanda ta ceto wani Jariri da aka yi garkuwa da shi a jihar Imo

Legit.ng ta fahimci cewa, ana sa ran za a kawo karshen kalubale na fataucin muggan kwayoyi gami da ta'ammali da su da zarar majalisar ta zartar da wannan dokoki kafin 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel